Malamin Addini Ya Ragargaji Tinubu bayan Ganawa da Gwamnan Bauchi

Malamin Addini Ya Ragargaji Tinubu bayan Ganawa da Gwamnan Bauchi

  • Shahararren Fasto, Johnson Suleman ya danganta matsalolin tattalin arzikin Najeriya da zaben 2023, yana cewa rashin kyakkyawan zabi ya jawo haka
  • Johnson Suleman ya yi kakkausar suka kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu, musamman kan yadda aka tafiyar da bangaren man fetur
  • Gwamna Bala Mohammed ya ce manufofin Tinubu sun jefa Najeriya cikin mummunan hali, yana mai jan hankalin kan daukar tsauraran matakai
  • Wani matashi a jihar Gombe ya zantawa Legit cewa babu tabbas a kan 'yan Najeriya za su nuna sun dauki darasi a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Babban Faston cocin Omega Fire Ministries, Johnson Suleman ya ce wahalhalun rayuwa da 'yan Najeriya ke ciki sakamakon mummunan zaben shugabanni ne a 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Fasto Johnson Suleman ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka shirya a jihar Bauchi na tsawon kwanaki biyu.

Johnson Suleman
Fasto Suleman ya bukaci 'yan Najeriya su dauki darasi a 2027. Hoto: APostle Johnson Suleman|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Hadimin gwamnan jihar Bauchi a fannin yada labarai, Lawal Muazu ya wallafa a Facebook cewa Faston ya ziyarci gidan gwamnati tare da gana wa da gwamna Bala Mohammed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alakar wahalar rayuwa da zaben 2023

Da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin Bauchi, Fasto Suleman ya yi kakkausar suka kan yadda 'yan Najeriya suka zabi shugabanni ba tare da lura da cancanta ba.

"'Yan Najeriya sun cancanci halin wahalar rayuwa da suke fuskanta a halin yanzu. Kafin zabe, mun yi kira, mun yi gargadi, amma mutane sun yi biris,"

- Fasto Johnson Suleman

Ya zargi shugaba Bola Tinubu da rashin gabatar da ingantacciyar manufa kafin zabe, yana mai cewa ya dogara ne kawai da zancen"Emilokan."

Kara karanta wannan

Rikicin Tinubu da gwamnan Bauchi: Minista ya fadi dalilin rashin jituwa

Sukar manufofin gwamnatin Bola Tinubu

Fasto Suleman ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Tinubu suna kara jefa tattalin arzikin kasar cikin mummunan hali, musamman kan bangaren man fetur.

"An lalata bangaren man fetur. A shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa, ba zan yi mamaki ba idan Najeriya ba ta farfado ba. Abu daya kawai za mu iya yi yanzu shi ne addu'a,"

- Fasto Suleman

Jaridar Punch ta wallafa cewa Faston ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dauki darasi daga abin da ke faruwa a yanzu domin guje wa irin wannan kuskuren a zaben shekarar 2027.

Bala Mohammed ya soki gwamnatin Tinubu

A nasa bangaren, Gwamna Bala Mohammed ya yi suka kan manufofin gwamnatin tarayya, yana mai cewa babu hangen nesa a cikin su.

Sanata Bala Mohammed ya ce tsare tsaren shugaba Tinubu ba su da kyakkyawar manufa kuma sun jefa Najeriya kan hanyar lalacewa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya suka fada bayan Buhari ya yi kyautar daloli

Gwamnan ya bayyana cewa yana goyon bayan tsare tsaren, amma ya ce gyaran da ake bukata ya kasance wanda zai amfani kasa gaba daya, ba wai wanda zai kara dagula al'amura ba.

Bala Mohammed zai cigaba da sukar Tinubu

Gwamna Mohammed ya jaddada cewa zai ci gaba da yin suka kan duk wata manufa da ba za ta amfani al'ummar Najeriya ba.

Sanata Bala Mohamed ya ce 'yan Najeriya sun cancanci samun cigaba, kuma ba zai yi shiru ba idan ya ga kura-kuran gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa ya kamata a rika fifita bukatun al'umma wajen tsara manufofin gwamnati domin tabbatar da samun ci gaba mai dorewa.

Legit ta tattauna da matashi

Wani matashi a jihar Gombe, Dauda Idris ya zantawa Legit cewa shi a karan kansa ya dauki darasi a kan abin da ke faruwa a yanzu, amma babu tabbas a kan sauran 'yan kasa.

Kara karanta wannan

Jawabin Abba Kabir Yusuf a wajen maulidin Kano da aka so hanawa

"Duk da cewa akwai sauran lokaci da gwamnati za ta iya daukar wasu matakai da za su iya canza ra'ayin 'yan kasa, ni kam na gama yanke matsaya a kan 2027."
"Amma lura da yadda kowa yake da ra'ayin kansa, ba za mu iya cewa kowa ya koyi darasi ba. Domin abin da zai faranta ran wasu, shi zai bakanta ran wasu."

- Dauda Idris

Gwamna ya zargi Tinubu da rusa 'yan adawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce Bola Tinubu na amfani da wata hanya domin samun nasara a 2027.

Gwamna Bala Mohammed ya bukaci shugaban kasar da ya daina amfani da ministocinsa wajen sukar 'yan adawa ba tare da wani dalili ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng