Sau 6 ina karance Qur'ani, kuma na yadda Musulunci addinin zaman lafiya ne - Fasto Suleiman
- Shugaban cocin Omega Power Ministries ta duniya, Fasto Johnson Suleman ya ce ISWAP ba musulunci suke yi ba
- Faston yace ya karanta Qur'ani sama da sau shida amma bai ga inda aka umarci wani musulmi ya kashe wani mutum
- Ya kushe kisan da ISWAP suka yi wa Kiristoci 11 kuma yace ba musulunci bane
Shugaban cocin Omega Power Ministries ta duniya, Fasto Johnson Suleman ya bayyana ra'ayin shi a kan matsalolin da ake samu a fannin addinin Musulunci.
Sanannen abu ne cewa kiristoci da wasu kungiyoyinsu suna kallon addinin Musulunci a matsayin addinin tashin hankali saboda ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'addan da suke fitowa suke ikirarin cewa addinin suke yi.
Amma kuma wani fasto ya fito kuma yayi magana ta wani bangare daban. A yayin da ISWAP suka halaka Kiristoci 11 a kwanakin baya, faston ya bayyana cewa Musulunci addini ne na lumana kuma da kanshi ya karanta Qur'ani sama da sau shida. Ya tabbatar da cewa littafin bai taba umartar wani ya kashe mutum dan uwan shi ba.
KU KARANTA: Amfanin cin dafaffen kwai guda 7 a jikin mutum
A kalaman shi: "Qur'ani yace duk wanda ya kashe rai daya tamkar ya kashe dukkan mutane ne. ISWAP shaidanu ne kuma Ubangiji zai hukunta su. Kun cire kan Kiristoci 11 ko? A shekarun da suka gabata, na karanta Qur'ani sama da sau shida. Babu musulmi nagari da zai kashe wani mutum. Musulunci addini ne na salama".
Kungiyar Kiristoci ta kasa da Shugaban kasa Buhari sun kushe kisan aka yi wa Kiristocin a kwanakin baya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng