Innalillahi: Babban Basarake Ya Rasu Jim Kadan Bayan Dawowa Daga Sallar Idi

Innalillahi: Babban Basarake Ya Rasu Jim Kadan Bayan Dawowa Daga Sallar Idi

  • An shiga wani irin yanayi bayan samun labarin rasuwar babban basarake a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka
  • Marigayin da ke sarautar Isolo a jihar ya rasu ne a yau Laraba 10 ga watan Afrilu bayan ya dawo daga sallar idi
  • Shugaban karamar hukumar Isolo a jihar Legas, Olasoju Adebayo shi ya tabbatar rasuwar basaraken inda ya ce za a binne shi da yammacin yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - An shiga jimami bayan rasuwar Osolo na masarautar Isolo a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka ya na da shekaru 64.

Basaraken ya rasu ne a yau Laraba 10 ga watan Afrilu a Legas jim kadan bayan dawowa daga sallar idi, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Daso, an sanar da mutuwar wata matashiyar jarumar fina-finai

Basarake ya rasu bayan dawowa daga sallar idi
Basarake a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka ya rasu bayan gudanar da sallar idi. Hoto: Oba Kabiru Agbabiaka.
Asali: Facebook

Yaushe za a binne marigayin a Legas?

Shugaban karamar hukumar Isolo a jihar Legas, Olasoju Adebayo shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba 10 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adebayo ya ce za a binne marigayin da misalin karfe 4 na yammacin yau kamar yadda addinin Musulunci ya koyar, cewar Vanguard.

Sanarwa kan mutuwar basaraken a Legas

"Na samu umarni daga mai girma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da na sanar da ku rasuwar basaraken Isolo, Oba Kabiru Agbabiaka."
"Basaraken ya rasu a yau Laraba 10 ga watan Afrilu ya na da shekaru 64 a duniya."
"Za a binne shi da misalin karfe 4 na yamma a yau a fadarsa da ke kan titin Akinbaye kamar yadda addinin Musulunci ya koyar."
"Muna masa addu'ar ubangji ya masa rahama ya kuma gafarta masa."

Kara karanta wannan

An rage mugun iri bayan hallaka kasurgumin dan ta'adda da 'yan bindiga suka yi fada

- Olasoju Adebayo

Tsohon alkalin kotun daukaka kara ya rasu

Kun ji cewa tsohon alƙalin kotun ɗaukaka ƙara, Ahmad Olanrewaju Belgore ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 71 a duniya.

Kamaludden Gambari, shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Kwara shi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta a ranar Talata 9 ga watan Afrilu.

Marigayin ya yi ritaya a matsayin alƙalin kotun ɗaukaka ƙara a ranar 18 ga watan Afrilun 2023, bayan ya kai shekara 70.

Asali: Legit.ng

Online view pixel