Zababben gwamnan Ekiti Biodun Oyebanji ya yi godiya ga al’ummar jiharsa

Zababben gwamnan Ekiti Biodun Oyebanji ya yi godiya ga al’ummar jiharsa

  • Zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi jawabinsa na farko tun bayan lashe zaben ranar Asabar, 18 ga watan Yuni
  • A cikin wani dan takaitaccen sako, Oyebanji ya nuna godiya ga al’ummar jihar Ekiti kan goyon bayan da suka bashi tare da zabarsa
  • Zababben gwamnan ya wallafa jawabin godiyar ne a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, jim kadan bayan hukumar zabe ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Kasa da sa’o’i 12 bayan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya saki jawabinsa na farko.

Oyebanji ya saki jawabin nasa ne a takaice a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, jim kadan bayan sanar da shi a matsayin zababben gwamnan na jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Gwamnan Ekiti: Ba za mu karbi kudi ba, masu zabe sun dage, sun zargi APC da hauro da mutane don su yi zabe

Biodun Oyebanji a taron kamfen dinsa
Zababben gwamnan Ekiti Biodun Oyebanji ya yi godiya ga al’ummar jiharsa Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Sabon gwamnan wanda ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi godiya ga daukacin al’ummar jihar Ekiti da suka zabe shi har ya kai ga lashe zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yuni.

Ya rubuta a shafin nasa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Nagode maku Ekiti Kete.”

PM News ta kuma kawo cewa Oyebanji ya wallafa hotonsa dauke da tsintsiya wacce ita ce alamar jam’iyyar APC a wajen babban gangamin kamfen din jam’iyyar da aka yi a ranar Talata a Ado-Ekiti.

Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari

A gefe guda, Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya taya dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin inuwar Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Biodun Oyebanji, murnar lashe zaben da ya yi.

Shugaban kasar ya kuma taya shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da kwamitin aiki na jam’iyyar murna kan wannan nasara wanda ita ce ta farko a karkashin sabuwar shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Lawan ya tsallake rijiya da baya, sunansa ya maye gurbin na Machina a matsayin dan takarar sanata na APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel