'Yan Bindiga Sun Shiga Kananan Hukumomi 40 a Najeriya, Basarake Ya Yi Gargadi

'Yan Bindiga Sun Shiga Kananan Hukumomi 40 a Najeriya, Basarake Ya Yi Gargadi

  • Jagoran Yarabawa, Gani Adams, ya ce ‘yan ta’adda sun shiga akalla kananan hukumomi 40 a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Adams ya bayyana cewa sun dade suna gargadin gwamnoni kan matsalar amma ba a samu hadin kai ko an saurari gargadinsu ba
  • Ya ce kungiyoyin OPC da mafarauta za su hada kai domin dakile hare-haren masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga a yankunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lagos - Aare Ona Kakanfo na kasar Yarabawa, Gani Adams, ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun yi kutse cikin akalla kananan hukumomi 40 a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Adams ya ce a cikin shekaru biyu da suka gabata yana ta gargadi kan yadda ‘yan ta’adda ke kara shiga yankin, amma ba a dauki matakin da ya dace ba.

Kara karanta wannan

An nemi a kama Sheikh Ahmad Gumi game da kalamansa kan ta'addanci a Najeriya

Gani Adams ya yi gargadin cewa 'yan bindiga suna kan kutsawa kananan hukumomin shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.
Aare Ona Kakanfo na kasar Yarabawa, Gani Adams da ya yi magana kan matsalar tsaro a Kudu maso Yamma. Hoto: @kwaraKogi
Source: Twitter

Gani Adams ya yi gargadi kan tsaro

Babban basaraken ya bayyana hakan ne a yayin da yake yin wata hira da jaridar The Punch a ranar 20 ga watan Mayu, 2026.

A cewarsa, akwai kananan hukumomi 137 a yankin Kudu maso Yamma, kuma sun gano dimbin ‘yan ta’adda a wasu daga cikinsu.

“Muna da kananan hukumomi 137 a Kudu maso Yamma, kuma mun gano dimbin ‘yan ta’adda a akalla kananan hukumomi 40,” in ji Gani Adams.

Ya ce sun boye wasu bayanan sirri ne saboda sun fi ganin hada kai da gwamnatocin jihohi zai fi amfani wajen magance matsalar tsaro.

Kokarin basarake kan tsaron Kudu

Adams ya ce sun yi kokarin hada kai da gwamnoni a yankin tsawon shekaru biyu amma hakan bai haifar da sakamako mai kyau ba.

"Shekaru biyu muna neman hadin kan gwamnatin jihohi. Wannan gwamnati ce da ta san ka san abubuwan da ke faru a fadin kasar Yarabawa, har ma a wasu jihohin Arewa, amma duk da haka, ta ki yarda ta zauna da kai, ta saurare ka, ko ta ba ka wata gudunmawa, duk da hakkinta na samar da tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun far wa mutane bayan sun dawo daga sayayyar kayan Sallah a Katsina

"To a yanzu dai za ka sanya a ranka cewa gudunmawa daya za ka iya ba kasar Yarabawa, watau yin magana a kafafen watsa labarai, ka fadi dan abin da ka sani game da shigowar 'yan bindiga garuruwa, don za ka lalata wasu abubuwan idan ka fito ka saki dukkan bayanai."
Gani Adams ya ce sun kwashe shekaru 2 suna gargadar gwamnatoci kan matsalar tsaro amma ba a saurare su ba.
Aare Ona Kakanfo na kasar Yarabawa, Gani Adams da ya yi magana kan matsalar tsaro a Kudu maso Yamma. Hoto: Legit.ng
Source: Original

OPC za ta hada kai da mafarauta

Gani Adams ya kuma yi magana kan kokarin mafarauta wajen tunkarar masu garkuwa da dalibai da malamai a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Basaraken ya ce mafarautan ba su da cikakken iko ko kayan aiki masu yawa, amma suna da muhimmiyar rawa wajen tattara bayanan sirri, in ji rahoton The Cable,

A cewarsa, dukkan bangarorin kungiyar Oodua Peoples Congress (OPC) da sauran kungiyoyi za su hada kai domin yakar masu aikata laifuka a yankin.

“Dole ne kowa ya hada kai wajen yaki da wadannan miyagun mutane. Tsaro ba wai daukar manyan makamai kadai ba ne."

- Gani Adams.

Hare-hare sun addabi yankin Oyo

Tun da fari, mun ruwaito cewa, a ranar 15 ga watan Mayu, 2026 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantu da wasu al’ummomi a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Makarantun da abin ya shafa sun hada da makarantar naziri da firamare ta Baptist da ke Yawota, Community Grammar School da kuma makarantar firamare ta LA da ke Esin Ele.

Rahotanni sun kuma nuna cewa ana yawan samun hare-haren ‘yan ta’adda a wasu garuruwan da ke jihar Ondo a ‘yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com