Makiyaya Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Oyo, Sun Jikkata Malamai

Makiyaya Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Oyo, Sun Jikkata Malamai

  • Wasu makiyaya sun kutsa kai cikin makarantar Sakandire a yankin ƙaramar hukumar Oriire, jihar Osun da safiyar Alhamis
  • Ganau ya ce makiyayan sun shiga gonakin makarantar, da aka musu magana suka farwa malamai da ɗalibai
  • Shugabar makarantar ta ce sun kira jami'an 'yan sanda suna kan hanyar zuwa don magance matsalar

Oyo - Wasu mahara da ake kyautata zaton Makiyaya ne, ranar Alhamis, sun kai farmaki wata Makarantar Sakandiren gwamnati a jihar Oyo, sun jikkata ɗalibai da Malamai.

Vanguard ta gano cewa maharan makiyayan sun kutsa kai cikin makarantar Community Grammar School da ke garin Alaropo Nla a ƙaramar hukumar Oriire, jihar Oyo.

Makiyaya.
Makiyaya Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Oyo, Sun Jikkata Malamai Hoto: vanguard
Asali: Twitter

Wani ganau da ya shaida duk abinda ya faru ya ce, makiyayan da suka kai mutane sama da 20 sun shiga makarantar tare da dabbobinsu kana suka raunata wasu ɗalibai da malamai.

Kara karanta wannan

Toh fa: Mutumin da ya ba da maniyyinsa aka haifi yara sama da 500 zai fuskanci tuhumar kotu

Wasu daga cikin Malamai da ɗalibai da lamarin ya shafa, cikinsu har da wani mai suna Mista Paul Olabode, makiyayan sun yanke su da wuƙake da Adduna, wasu kuma sun karye a kafafu da hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar ta ce makarantar ta gama ayyukan safiya kuma ɗalibai sun fara haramar shiga azuzuwa domin ci gaba da jarabawar karshen zango na biyu lokacin da makiyayan suka kutsa kai.

Ya ce da fari, makiyayan sun shiga gonakin da ke cikin makarantar tare da Dabbobinsu suna kiwo, suna cin ciyayi da amfanin cikin gonakin.

A yunkurin da Malaman suka yi tare da ɗalibai na korar makiyayan ne suka gamu martani mara kyau, wanda ya illata wasu daga cikinsu, inji rahoton Sahara Reporters.

Shugabar makarantar Sakandiren da abun ya afku, Misis Grace Alamu, ta tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar salula, ta ce tuni suka kai rahoto ga yan sanda.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

"Ina kan hanyar zuwa makaranta, 'yan sanda zasu zo makarantar da safen nan," inji ta.

Duk wani yunkuri na tabbatar da lamarin daga bakin jami'in hulɗa daa jama'a na hukumar yan sandan Oyo, Adewale Osifeso, ya ci tura har kawo yanzu.

Jiragen Helikwafta 2 Na Rundunar Soji Sun Yi Hadari

A wani labarin kuma Jiragen Rundunar Soji Sun Yi Mummunan Hatsari, Mutane da Yawa Sun Mutu

Mahukunta a ƙasar Amurka sun tabbatar da cewa wasu jiragem rundunar soji guda biyu sun gamu da hatsari yayin da suke shawagin ɗaukar hoto a Kentucky.

Ana fargabar da yawan mutanen cikin jiragen biyu sun rasa rayukansu yayin da jami'an tsaro suka fara bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel