Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri

Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri

- Hukumar Hisbah ta Yauri a jihar Kebbi ta haramta da kuma wajabta wasu sabbin dokoki

- Daga yanzu hukumar ta tilastawa duk Limamin da zai daura aure ya tabbatar da an gabatar masa da wasu gwaje-gwaje na ma'auratan

- Ta kuma hana matasa yin wasu irin shiga da ba na mutunci ba a yankin

Hukumar hisbah a garin Yauri da ke jihar Kebbi ta kafa wasu sabbin dokoki ga al’umman jihar a kokarinta na dinke wasu baraka tare da ladabtar da mutanenta.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta kuma wajabtawa limamin da zai daura aure ya tabbatar da an gabatar masa da sakamakon gwaje gwaje da ma’auratan suka yi daga babban asibiti.

Ya kuma haramtawa matasa saka wandon sagin da askin banza.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe jigon PDP, sun yi garkuwa da yayansa mata su 3

Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri
Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri
Source: Twitter

Jawabin ya zo kamar haka:

“Abubuwan da Hisbah ta hana aikatawa cikin garin Yauri

"1. Gwaji ga Ma’aurata

"Namiji: Gwajin Kanjamau (HIV/AIDS), gwajin Anta (Hypatitis).

"Macce: Gwajin Kanjamau (HIV/AIDS), gwajin anta (Hypatitis), gwajin ciki.

"2. An hana sa wandon sagin

"3. An hana askin banza

"4. An hana P.E.S.

"5. Ba’a kai karfe 6 na marance wajen talla cikin kasuwa

"6. Ba’a daukan mata biyu a mashin sai da lalura

"7. Ba’a awo da kwanon da ya lankwashe

"8. An hana kide-kiden D.J. Da Wasigidi

"9. An hana buga 9jaBet

"Wajibi ne duk Limamin da zai daura Aure ya tabbatar da an gabatar masa da takardar sakamakon gwaje-gwajen da aka yi daga babban likita na babbar asibiti (General Hospital) kafin a daura aure.

"Wanda duk aka samu ya sabama wannan dokan sa’a gabatar dashi gaban shari’a.

"Daga karshe muna rokon Allah ya karemu da miyagun kaddarori."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hawaye sun kwaranya yayinda Shugaban APC a Lagas ya mutu (hoto)

A wani labarin, Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Gabon ta yi wa wani dattijo da ya nuna yana kaunarta sha tara ta arziki.

Jarumar ta yi wa dattijon wanda ba a bayyana sunansa ba kyautar kudi har naira dubu dari biyu.

Hakan ya faranta ran tsohon har ya bayyana cewa ya janye tare da yi mata fatan alkhari da tarin addu’o’i.

on sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel