Gobarar da ta kona shaguna sama da 150 a Funtua (hotuna)

Gobarar da ta kona shaguna sama da 150 a Funtua (hotuna)

- Gobara ta tashi a wata kasuwa da ke garin Funtua a daren ranar Laraba, 23 ga watan Disamba

- Tashin gobarar ta yi sanadiyar konewar shaguna fiye da 150

- An jajantawa yan kasuwar asarar da suka yi tare da kira ga gwamnatin jihar Katsina a kan ta kawo masu agaji

Wata gobara da ta tashi da misalin ƙarfe 8 na daren ranar Laraba, ta yi sanadin ƙona shaguna sama da 150 a garin Funtua, jihar Katsina.

Wakilin Legit.ng Hausa, Sani Hamza Funtua wanda ya ziyarci kasuwar da gobarar ta faru, ya ruwaito cewa, gobarar ta jawo asarar dukiyar ƴan kasuwa, da kuɗin su ya zarce miliyoyin Naira.

Da ya ke zantawa da jaridar Legit.ng Hausa, shugaban ƴan kasuwar na bakin babban asibitin Funtua (SMASH), Alhaji Mujitafa Ibrahim, ya bayyana cewa, wannan ne karo na kusan uku da gobarar ta ke tashi a kasuwar, lamarin da ke jefa ƴan kasuwar a wani hali.

Gobarar da ta kona shaguna sama da 350 a Funtua (hotuna)
Gobarar da ta kona shaguna sama da 350 a Funtua
Asali: Original

KU KARANTA KUMA: Mawakin Buhari Rarara ya shiga matsala kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa

Alhaji Mujitafa, wanda shagunan sa uku suka ƙone sakamakon gobarar ya sanar da cewa, gobarar ta kama ne sakamakon wutar lantarki da ta kama shago ɗaya.

Daga bisani kuma sai gobarar ta mamaye sauran shagunan da ke kasuwar inda ta ƙone shaguna sama da 150.

"Asarar da muka yi ba ta misalto, sama da shaguna 150 suka ƙone, kenan za a iya ƙiyasin sama da Naira miliyan 50 zuwa 100 ne aka yi asarar su a gobarar."

Shi ma da yake jawabi, mataimakin shugaban ƴan kasuwa na ƙaramar hukumar Funtua, Alhaji Kabir Sa'idu Rawayau, ya jajanta wa ƴan kasuwar da gobarar ta shafa.

Ya roƙi gwamnatin jihar Katsina da ta taimakawa ƴan kasuwar.

"Mun sha samun irin wannan matsalar a kasuwar bakin asibitin Funtua, duka bai wuce shekara ɗaya irin wannan gobara ta faru a kasuwar ba, don haka, muna roƙon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da ya dubi ƴan kasuwar da wannan iftila'i ya shafa, ya taimaka masu."

Alhaji Kabir Rawayau, ya kuma roƙi ƴan kasuwa da su kasance masu sanya idanuwa sosai a wayoyin da suke jan wutar NEPA da su, da kashe ƙwayaye ko soket in an tashi kasuwa.

Wasu ƴan kasuwar da gobarar ta shafa, sun roƙi gwamnatin Katsina, da ta kai masu ɗauki, sakamakon mawuyacin halin da za su iya shiga sanadiyyar asarar dukiyoyin su a gobarar.

KU KARANTA KUMA: An nemi Bala Mohammed ya shiga tseren shugaban kasa a 2023

Gobarar da ta kona shaguna sama da 350 a Funtua (hotuna)
Gobarar da ta kona shaguna sama da 350 a Funtua
Asali: Original

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta isa kasuwar bayan samun rahoto cikin gaggawa, sai dai ƙarancin ruwan da aka samu, ya sa gobarar ta ƙona sama da shaguna 150.

A wani labarin na daban, wasu 'yan bindiga a ranar Laraba da yammaci sun kai wa dakarun soji hari a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi inda suka kashe sojin ruwa biyu.

Jaridar Tribune Online ta tabbatar da cewa an kai wa sojin hari wurin karfe 7 na yammacin ranar Laraba a Okene yayin da suke shirin fara aiki.

Shugaban karamar hukumar Okene, Abdulmumin Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel