Jami'ar Baze Ta Karrama 'First Lady' Maryam Babangida Shekaru 14 Bayan Rasuwarta

Jami'ar Baze Ta Karrama 'First Lady' Maryam Babangida Shekaru 14 Bayan Rasuwarta

  • Jami’ar Baze da ke Abuja ta karrama wasu ‘yan Najeriya biyu, Maryam Babangida da Mai shari’a Mohammed Bello da shaidar digirin girmamawa
  • Mrs Babangida matar tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ce, yayin da Mista Bello ya kasance alkalin alkalan Najeriya daga 1987 zuwa 1995
  • Jami’ar Baze, ta samu gagarumin ci gaba, ciki har da bunkasa kwasa-kwasan ilimi daga 72 a shekarar 2022 zuwa 102

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Jami’ar Baze da ke Abuja ta karrama wasu ‘yan Najeriya biyu, Maryam Babangida da Mai shari’a Mohammed Bello.

Yayin da Maryam ta samu digirin girmamawa a fannin kimiyya, shi kuma mai shari'a ya samu lambar yabo ta digirin girmamawa kan wasiku.

Kara karanta wannan

Zabe ya kammala a Kogi, INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe, ya fi kowa adadin kuri'u

Maryam Babangida, Justice Mohammed Bello
Jami’ar Baze ta karrama Maryam Babangida da Mai Shari’a Mohammed Bello da Lambobin girmamawa Hoto: Wikipedia
Asali: UGC

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Mrs Babangida matar tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ce, yayin da Mista Bello ya kasance alkalin alkalan Najeriya daga 1987 zuwa 1995.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarorin da jami'ar Baze ta samu

Mukaddashiyar shugaban jami'ar, Farfesa Kathleen Okafor, ita ce ta bayar da lambobin yabo ga jiga-jigan ‘yan Najeriya biyun a karshen makon da ya gabata, a wajen taron jami'ar karo na 10 da aka gudanar a Abuja.

Da take magana a wajen taron, Mrs Okafor ta ce jami’ar ta samu gagarumin ci gaba, ciki har da bunkasa kwasa-kwasan ilimi daga 72 a shekarar 2022 zuwa 102.

Mrs Okafor ta ce wannan ya kunshi kwasa-kwasan karatun digiri 43, kwasa-kwasan digiri na biyu (PGD da MSc) 41 da kuma kwasa-kwasan PhD 18.

Jami'o'i su sake fasalin shirye-shiryensu - Mrs Okafor

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wasu ‘yan bindiga sun bindige shugaban jam’iyyar siyasa a jihar Anambra

Mukaddashiyar shugaban jami’ar, ta kuma ce dole ne mata su taka rawa wajen ganin sun kasance cikin fafutukar farfado da tattalin arziki domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Ta ce, ya zama wajibi daga yanzu jami'o'i su mayar da hankali ga bangaren ilimin da ya dace da da'ar jama'a, yaki da kisan kare dangi da talauci, keta doka da sauransu.

Rasuwar Maryam Babangida

Allah ya yiwa Hajiya Maryam Babangida.rasuwa ranar 27 ga Disamba, 2009, tana mai shekaru 61.

Ta rasu ne a jami'ar California dake Amurka bayan fama da cutar kansa, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel