Sojoji Sun Kama Fasinjoji da Mugayen Makamai a Hanyar Kaduna zuwa Jos

Sojoji Sun Kama Fasinjoji da Mugayen Makamai a Hanyar Kaduna zuwa Jos

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wata mota a makare da makamai masu hadarin gaske a hanyar Manchok–Jos
  • An kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a safarar makaman da ake hasashen ana shirin ta'addanci da su
  • Jami'an tsaron sun yi nasarar kwato harsasai 569 da sauran kayan fashewa da aka duƙunƙune a cikin motar ɗauke da fasinjoji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun nuna cewa dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wasu mutane tare da kwace makamai da ake zargin na tayar da bam a yankin hanyar Kaduna zuwa Filato.

A cewar majiyoyin, lamarin ya faru ne da 11:45 na safe a ranar 16 ga Afrilu, 2026, lokacin da sojojin da ke aiki a Manchok, kusa da makarantar sakandaren kimiyya ta maza.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban da suka je yin jarabawar JAMB

Sojoji sun kama makamai
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Getty Images

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa sojojin sun tare wata motar haya kirar Opel wagon mai launin shuɗi, inda suka yi gam da katar da makaman.

Sojoji sun kama mota da makamai

Rahoton ya ce motar na dauke da fasinjoji bakwai a lokacin da aka tsaida ta domin binciken yau da kullum da aka saba yi a hanyar.

A yayin binciken ne jami’an tsaro suka gano wasu abubuwa masu yawa da ake zargi na da alaka da ayyukan ta’addanci an ɓoye su.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da harsasai 569 na bindigar yaki da jirgi mara matuki da, wani kan makami mai linzami.

Sauran sun haɗa da harsasan AK-47 da babu komai a ciki, da wasu sassan kayan hada abubuwan fashewa. Haka kuma an samu wasu wayoyin hannu da aka lalata.

Sojoji sun fara bincike

Binciken farko ya nuna cewa direban motar, mai suna Khalifa Bawa, ya yi ikirarin cewa kayan wani ne da aka ba shi saƙo, amma ya kasa bayar da sunan wanda ya aiko da su ko wanda za a kai wa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan sojojin Najeriya, an yi asarar rayuka a Borno

Sojoji sun fara binciken fasinjoji
Dakarun sojoji a yayin wani fareti Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Bayan haka, jami’an tsaro sun kama dukkanin mutanen da ke cikin motar tare da tsare su domin ci gaba da bincike.

Ana sa ran za a mika wadanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu idan an samu hujjoji.

Majiyoyi daga rundunar sojoji sun bayyana cewa dakarun na ci gaba da zama cikin shiri a yankin, inda suke gudanar da ayyuka ba tare da gajiyawa ba domin dakile safarar makamai.

Sun kuma jaddada cewa irin wadannan samame na daga cikin kokarin da hukumomin tsaro ke yi na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Ƴan ta'adda sun far wa sojoji

A baya, mun wallafa cewa wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun kashe sojoji hudu da mace daya a wani hari da suka kai garin Mussa, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

Dakarun bataliya ta 115 sun nuna bajinta wajen dakile yunkurin maharan na shiga cikin gari domin yin barna, amma an rasa rayukan wasu daga cikin sojojin.

Mazauna yankin sun shiga fargaba yayin da aka riƙa musayar wuta na tsawon mintuna 30 kafin sojoji su fatattaki maharan gaba daya, a dawo da zaman lafiya yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng