Sabon Rikici: Trump Ya Yi wa Netanyahu Cin Fuska kan Lebanon da Syria

Sabon Rikici: Trump Ya Yi wa Netanyahu Cin Fuska kan Lebanon da Syria

  • Shugaba Donald Trump ya gargadi Benjamin Netanyahu ya fara janye sojojin Isra'ila daga kudancin Siriya da Lebanon
  • Rahoto ya nuna cewa Netanyahu ya ce janye sojojin zai iya shafar tsaron Isra'ila, saboda haka bai amince da buƙatar ba
  • Amurka ta ce ta dade tana ƙoƙarin sasanta yarjejeniyar tsaro tsakanin Isra'ila da Siriya, amma ba a cimma matsaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - An rawaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya buƙaci Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da ya fara janye sojojin Isra'ila daga kudancin Siriya da Lebanon.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da takun saka a Gabas ta Tsakiya, musamman tsakanin kasashen Amurka da Iran.

Benjamin Netanyahu da Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump na magana da Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya gargadi Netanyahu

Times of Israel ta wallafa cewa a wata tattaunawa, Trump ya gargadi Netanyahu cewa ci gaba da kasancewar sojojin Isra'ila a yankunan Siriya na haifar da tashin hankali wanda zai iya rikidewa zuwa sabon rikici.

Kara karanta wannan

Kalaman Sanata Graham na karshe sun bayyana kafin mutuwarsa a Amurka

An ce Trump ya shaida masa cewa:

"Ba sa son ku kasance a can. Ya kamata ku sake janye dakarunku."

Rahoton ya nuna cewa shugaba Donald Trump ya kuma mika irin wannan buƙata dangane da kasar Lebanon.

Netanyahu ya ki yarda da Trump

An ce Netanyahu ya nuna rashin amincewarsa da wannan buƙata, yana mai cewa hakan yana da alaƙa da bukatun tsaron Isra'ila.

Rahoton ya ƙara da cewa, tsawon watanni gwamnatin Amurka na ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsaro tsakanin Isra'ila da Siriya, amma daga bisani ta fahimci cewa Netanyahu ba ya shirye da hakan.

Ofishin Firaministan Isra'ila ya bayyana a makon da ya gabata cewa a lokacin tattaunawar, Netanyahu ya jaddada bukatar samar da sojoji a kan iyakokin Isra'ila.

Fadar White House kuwa ta ƙi yin tsokaci kan cikakken abin da suka tattauna, sai dai ta yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Trump da Netanyahu.

Harin da aka kai Lebanon
Wani waje da Isra'ila ta kai hari a Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Alakar Isra'ila da Lebanon

A ranar Talata, an gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawar kai tsaye tsakanin Isra'ila da Lebanon a birnin Rome ƙarƙashin jagorancin Amurka, inda Jakadan Isra'ila a Amurka, Yechiel Leiter, ya halarta.

Kara karanta wannan

A karo na 3 a jere, Amurka ta kai munanan hare hare kan ƙasar musulunci ta Iran

Mai magana da yawun ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce tattaunawar ta gudana cikin yanayi mai kyau kuma ta haifar da sakamako mai kyau.

Times of India ta rahoto ya ƙara da cewa:

"Dukkan ɓangarorin suna da sha'awar ci gaba. Za a ci gaba da tattaunawar gobe."

A yayin tattaunawar, an tattauna yadda za a aiwatar da matakin farko na janye sojojin Isra'ila daga yankunan Kudancin Lebanon.

Za a kai karar Najeriya ga Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani kamfanin Amurka mai alaka da Atiku Abubakar ya ce zai kai karar Najeriya wajen Donald Trump.

Kamfanin ya yi magana ne bayan gwamnatin Bola Tinubu ta kama Adeniyi Adeyemi da ake zargi ya kafa ma'aikatar bogi.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa a yanzu haka ya fara tattaunawa da wasu 'yan majalisar Amurka kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng