Kamfanin Dangote Sinotruk Ya Kafa Tarihi, Ya Kaddamar da Babbar Mota Irinta Ta Farko a Najeriya
- Kamfanin Dangote Sinotruk ya kaddamar da motar dakon kaya mai amfani lantarki ta farko da aka hada a gida Najeriya
- Motar na da batirin wutar lantarki mai karfin 100 KWH, injin 95 kW da kuma damar tafiyar kilomita 200 kafin bukatar sake caji
- Kamfanin ya ce kaddamar da motar na daga cikin kokarinsa na bunkasa masana’antar kera motoci da rage gurbatar muhalli a Najeriya da Afirka ta Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - A wani mataki na bunkasa masana’antar kera motoci a Najeriya, kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited ya kaddamar da motar dakon kaya mai amfani da lantarki ta farko da aka ƙera cikin kasar.
Ya ce wannan ci gaba ya bude sabon babi a fannin amfani da makamashi mai tsafta, kera kayayyaki a cikin gida da kuma samar da hanyoyin sufuri masu dorewa a Najeriya da Afirka ta Yamma.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kaddamar da motar ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke kara kokarin sauyawa zuwa amfani da makamashi da hanyoyin sufuri masu tsafta.
An kaddamar babbar mota ta lantarki
An kaddamar da motar Dangote Sinotruk EV ne a masana’antar kera motoci ta kamfanin da ke Ikeja, jihar Legas.
Taron ya samu halartar manyan jami’an rukunin kamfanonin Dangote da Sinotruk, wakilan gwamnatin jihar Legas, masu ruwa da tsaki a masana’antar, kwastomomi, abokan hulda da sauran manyan baki.
Motar dakon kaya mai tsarin taya 4X2 na dauke da batirin wutar lantarki mai karfin 100 KWH, inji mai inganci da karfin 95 kW da kuma damar tafiyar kilomita 200. Haka kuma tana da babban wajen lodin kaya da wasu karin fasalulluka.
An kuma kaddamar da na’urar caji mai karfin 400 kW, wadda ke amfani da fasahar DC mai saurin caji tare da hanyoyin fitar da wuta guda biyu masu karfin gaske.
Kaddamar da motar na nuna yadda hadin gwiwar Dangote da Sinotruk ke fadada ayyukansa, daga kera motocin haya zuwa motocin da ke amfani da sababbin nau’ukan makamashi.
Amfanin kera motocin a Najeriya
Mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote Industries Limited, Devakumar Edwin, ya bayyana bullo da motocin kasuwanci na lantarki a matsayin wani muhimmin mataki a ci gaban hadin gwiwar kamfanonin biyu.
Ya ce hakan na nuna kudurin rukunin kamfanonin Dangote na rungumar sababbin fasahohi da za su samar wa abokan hulda da al’umma alfanun tattalin arziki, tare da taimakawa Najeriya wajen cimma manufofinta na kare muhalli.
Edwin ya ce an kafa hadin gwiwar Dangote da Sinotruk ne da babban burin gina kamfanin kera motocin kasuwanci na duniya a Najeriya, karfafa karfin kera motoci a cikin gida, musayar fasaha da samar da ayyukan yi.
"A yau mun shiga wani muhimmin mataki na gaba, a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke neman kasuwanci mai dorewa, wato motocin da za su taimaka wajen kare muhalli.
“Saboda haka, mun shiga fasahar CNG, yanzu kuma muna shiga fasahar motocin lantarki. Wannan fasaha ce da ke kawo sauyi a duk fadin duniya.”

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun afkawa masallata a sallar asuba a Zamfara, sun bindige hadimin gwamna
Edwin ya ce Dangote Sinotruk ta fara shirye-shiryen samar da kayayyakin more rayuwa da tallafin fasaha da ake bukata domin tabbatar da cewa za a iya amfani da motocin lantarkin yadda ya kamata a Najeriya.
“Wannan ya wuce kaddamar da sababbin motoci, yana nuna kudurinmu na kirkire-kirkire, amfani da makamashi mai tsafta da kuma makomar sufuri.”
Ya ce kamfanin na da niyyar amfani da girman kasuwar Najeriya, karfin masana’antunta da hazakar ’yan kasuwanta wajen samar da motoci ga sauran kasashen yankin.
Shugaban rukunin kamfanonin Sinotruk, Liu Wei, ya bayyana kaddamar da motar a matsayin wani muhimmin tarihi ga Najeriya, hadin gwiwar kamfanonin biyu da kuma masana’antar kera motoci a Afirka baki daya.
Ya ce motar dakon kaya mai nauyi ta lantarki wata hanya ce ta zahiri ta taimakawa Najeriya wajen cimma burinta na sauya sheka zuwa amfani da makamashi mai tsafta.
Liu ya ce motar ita ce ta farko mai amfani da sabon nau’in makamashi da aka kera a nahiyar Afirka, inda ya bayyana hakan a matsayin babban mataki na bunkasa kera motoci a cikin gida.
A cewarsa, wannan ci gaba ya yi daidai da manufofin Najeriya na dogon lokaci na rage hayakin da ke haddasa dumamar yanayi da kuma shirye-shiryen sauya tsarin makamashi.
Kun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin ƙara jarinsa a nahiyar Afirka daga dala biliyan 50 zuwa kusan dala biliyan 70.
Dangote ya kuma bayyana shirin samar da megawatt 10,000 na wutar lantarki a faɗin Afirka, wanda Najeriya za ta iya kasancewa cikin ƙasashen da za su amfana da wannan shiri.
Asali: Legit.ng


