Gwamnoni 19 Sun Bada Tallafi Mai Tsoka Ga Musulman da Sojoji Suka Jefa Wa Bam a Kaduna

Gwamnoni 19 Sun Bada Tallafi Mai Tsoka Ga Musulman da Sojoji Suka Jefa Wa Bam a Kaduna

  • Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun haɗa gudummuwar N180m sun baiwa mutanen da harin sojoji ya shafa a Tudun Biri
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ne ya faɗi haka bayan kammala taron da suka yi a Kaduna
  • Ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu tare da kira ga FG ta biya diyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamnonin arewa sun bayar da gudunmuwar Naira miliyan 180 ga wadanda harin bama-baman jirgin sojoji ya rutsa da su a kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.

Harin wanda rundunar sojijin Najeriya ta ce kuskure ne, ya yi ajalin mahalarta taron Maulidi sama da 100 tare da jikkata wasu da dama a kauyen da ke ƙaramar hukumar Igabi.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi matakin da suka ɗauka kan sojojin da suka kashe Musulmai a Kaduna

Gwamnonin arewa sun bada tallafi ga Tudun Biri.
Gwamnoni 19 Sun Bada Tallafi Mai Tsoka Ga Musulman da Sojoji Suka Jefa Wa Bam a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Gwamnoni 19 daga dukkan jihohin arewa sun bada wannan tallafi ga mutanen da ibtila'in ya afkamawa yayin taron da suka yi a Kaduna ranar Jumu'a, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a madadin takwarorinsa, shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya ce:

"Masu girma gwamnoni abokan aiki da sauran ƴan jarida, kamar yadda kuke gani, mun gabatar da gudummuwar mu ga waɗanda harin bam ya shafa a Tudun Biri da gwamnatin Kaduna domin ta tallafa musu."
“A madadin kungiyar gwamnonin Arewa, mun bayar da wannan tallafin ne domin gwamnatin jihar Kaduna ta yi amfani da kuɗaɗen wajen tallafa wa wadanda abin ya shafa."

Gwamnonin sun yi ta'aziyyar abinda ya auku

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya baiwa wadanda abin ya shafa da gwamnatin jihar Kaduna ƙarfin juriya da haƙuri bisa wannan rashi.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Gwamnonin Arewa sun hadu a Kaduna, karin bayani kan abin da za su tattauna

Haka nan kuma Gwamna Yahaya ya yi addu'ar Allah SWT ya gafartawa waɗanda suka rasu sakamakon wannan harin jirgi, wanda ya jefa bam har sau biyu.

Daga ƙarshe, Gwamnonin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta buya diyyar mutanen da lamarin ya shafa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wannan gudummuwa ta gwamnonin na zuwa ne bayan ƴan majalisar tarayya na arewa sun bada na su tallafin makonni bayan faruwar lamarin.

Muhimman Dalilai Uku da Ka Iya Sa a Tsige Gwamnan PDP

A wani rahoton Rigingimun siyasar jihar Ribas na ci gaba da ɗaukar hankali tunda yan majalisa 27 da ke goyon bayan tsohon gwamna, Nyesom Wike, suka fice daga PDP zuwa APC.

Garin ceton kansa daga tsarin siyasar uban gida da kuma makarantar siyasar Wike, ministan Abuja, Gwamna Fubara ya yi abinda ka iya raba shi da gadon mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262