Shugaban Kasa a Afirka Ya ba Yan Najeriya Hakuri kan Kalamansa, Ya Kira Sunan Tinubu
- Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya yi ƙarin haske kan abin da yake nufi game da Turancin yan Najeriya da ya kawo maganganu
- Ruto ya bayyana cewa an juya maganganunsa kan lamarim yana mai cewa ya furta su ne a tattaunawar sirri
- Ya ce bai yi niyyar raina ’yan Najeriya ba, sai dai yana yabon yadda ƙasashen Afirka ke amfani da Turanci cikin ƙwarewa da fahimta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nairobi, Kenya - Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya bayyana cewa an karkatar da maganganunsa da suka shafi Turancin ’yan Najeriya.
Kalaman Shugaba Ruto sun jawo ce-ce-ku-ce da kuma yawan suka a kafafen sada zumunta da ƴan Najeriya ke ganin an ci mutuncinsu.

Source: Getty Images
Ruto ya yi bayanin ne yayin taron zuba jari a harkar ma’adinai da aka gudanar a Nairobi ranar Talata, inda ya ce maganganun nasa an yi su ne cikin tattaunawar sirri, cewar TheCable.
Maganganun Shugaban Kenya da suka jawo magana
Tun farko dai shugaban ya jawo suka daga ’yan Najeriya lokacin da yake jawabi ga ’yan Kenya mazauna Italiya, inda ya yabawa tsarin ilimin ƙasarsa da harshen Turanci.
A yayin jawabin, Ruto ya ce tsarin ilimin Kenya yana da kyau kuma ’yan ƙasar na amfani da ɗaya daga cikin mafi kyawun Turanci a duniya baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa idan mutum ya saurari wani ɗan Najeriya yana magana, wani lokaci ba zai fahimci abin da ake faɗa ba sai an samu mai fassara.

Source: Facebook
Shugaba William Ruto ya fayyace abin da ya nufa
Sai dai yayin ƙarin bayani, inda ya ce yana aikawa da ’yan uwansa ’yan Najeriya gaisuwa, yana mai kiransu da surukansa cikin raha.
Ruto ya kuma ce a isar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da saƙon gaisuwarsa, yana mai cewa ya yi hakan ne cikin “Turanci mai kyau” domin kauce wa wata matsala.
Ya bayyana cewa yana magana ne da ’yan ƙasarsa a wani wuri cikin sirri, amma wani mutum ya yanke shawarar bayyana tattaunawar ga jama’a.
Shugaban ya ce manufarsa ita ce bayyana yadda ’yan Afirka gaba ɗaya ke iya Turanci sosai, musamman ma a ƙasashe irin Najeriya da ake amfani da ingantaccen Turanci.
A cewarsa, idan mutum bai iya Turanci sosai kamar yadda ake yi a Kenya ba, zai iya buƙatar mai fassara domin fahimtar yadda ’yan Najeriya ke magana da Turanci.
Ruto ya jaddada cewa wasu mutane sun karkatar da gaskiyar abin da ya faɗa, lamarin da ya sa aka samu rashin fahimta tsakanin kalamansa da abin da jama’a suka ɗauka.
Shugaban Kenya ya koka da mazan Najeriya
A wani labarin, an ji cewa Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya koka kan yadda 'ya'yansu mata da dama ke auren maza 'yan Najeriya, ciki har da 'yarsa, June Ruto.
A wani taro, Ruto cikin barkwanci ya ce matan Kenya na komawa zuwa Najeriya, yana tambayar dalilin da ya sa mazansu ba sa samun matan can.
Ruto ya ce yana goyon bayan auren ’yarsa, amma da wuya ya yarda, musamman da ta auri dan kabilar Igbo daga Najeriya a Yammacin Afirka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

