Shugaban Ƙasa a Afirka Ya Kunyata Najeriya a Turai, Ya Yi Mata Dariya kan Turanci
- Shugaban Kenya William Ruto ya kare tsarin ilimin kasarsa, yana cewa Turancinsu yana da kyau fiye da tunanin mutane
- Ruto ya kuma soki yadda wasu ‘yan Najeriya ke magana a Turance wanda kalamansa suka jawo maganganu a kafofin sadarwa
- Ya ce idan ka saurari dan Najeriya yana Turanci, kana bukatar mai fassara, yana mai jaddada cewa Kenya na da kwararrun ma’aikata masu inganci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rome, Italy - Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya kare tsarin ilimin kasarsa tare da yabawa kwarewar Turancinsu.
Shugaban kasar ya yi suka kan yadda wasu ‘yan Najeriya ke magana idan aka kwatanta da na su Turancin.

Source: Facebook
Shugaban Kenya ya soki Turancin yan Najeriya
Ruto ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga ‘yan Kenya mazauna Italiya, inda ya ce Turancinsu na daga cikin mafi kyau a duniya, cewar rahoton Punch.
Ya kara da cewa idan mutum ya saurari dan Najeriya yana magana da Turanci, zai iya kasa fahimta, yana mai cewa ana bukatar mai fassara.
Ruto ya ce Kenya na da manyan kwararru a fannoni daban-daban, amma ana bukatar kara horaswa domin inganta kwarewarsu da ci gaban kasa gaba daya.
Ana zargin Ruto na martani ne ga Tinubu
Duk da cewa bai ambaci wani kai tsaye ba, wasu sun danganta kalamansa da maganganun Shugaban Najeriya Bola Tinubu a farkon watan nan.
A yayin wata ziyara a Bayelsa, Tinubu ya ce duk da wahalar tattalin arziki, ‘yan Najeriya sun fi wasu kasashen Afirka, ciki har da Kenya, sauki.
Ya bukaci ‘yan kasa su gode wa Allah, yana mai cewa halin da wasu kasashe ke ciki ya fi na Najeriya tsanani a wannan lokaci.
Ƴan kasar Kenya da dama sun dura kan Tinubu game da kalamansa inda suke ganin hakan cin mutunci ne tare da ba shi shawarar ya ji da matsalolin da Najeriya ke ciki tukuna.

Source: Twitter
Martanin da mutane da dama ke yi
Wannan musayar kalamai ta jawo martani sosai a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka nuna rashin jin dadi da kalaman shugabannin.
Wasu sun zargi shugabannin da rage kimar kasashensu, yayin da wasu suka ce bambancin harshe ba ya nuna ingancin ilimi ko ci gaba, cewar BBC.
Haka kuma, Kenya ta fuskanci kalubalen tattalin arziki a baya-bayan nan, ciki har da zanga-zanga kan karin haraji a shekarar 2024 da sauran matsaloli da ba za a rasa ba.
Ruto ya koka kan mazan Najeriya
A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya koka kan yadda 'ya'yansu mata da dama ke auren maza 'yan Najeriya, ciki har da 'yarsa, June.
Ruto A wani taro, Ruto cikin barkwanci ya ce matan Kenya na komawa zuwa Najeriya, yana tambayar dalilin da ya sa mazansu ba sa samun matan can.
Ruto ya ce yana goyon bayan auren ’yarsa, amma da wuya ya yarda, musamman da ta auri dan kabilar Igbo daga Najeriya a Yammacin Afrika.
Asali: Legit.ng

