Jirgin Sama Ya Yi Mummunan Hatsari, Dukkanin Mutanen da ke Ciki Sun Mutu
- Akalla mutum 14 ne suka riga mu gidan gaskiya bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a kusa da birnin Juba na ƙasar Sudan ta Kudu
- Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasar (SSCAA) ta bayyana wasu dalilai da ta ce su ne suka janyo mummunan hatsarin jirgin
- Wannan na zuwa ne yayin da wani jirgi daban ya faɗi a ƙasar Paraguay yana ɗauke da miliyoyin daloli, wadanda mutane suka wawashe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sudan ta Kudu – Wani ƙaramin jirgin fasinja ya yi hatsari a ƙasar Sudan ta Kudu inda ya yi sanadin mutuwar dukkan mutane 14 da ke cikinsa.
Hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar (SSCAA) ta tabbatar da cewa jirgin ya faɗi ne da nisan kilomita 20 daga kudu maso yammacin babban birnin ƙasar, wato Juba, a safiyar ranar Litinin.

Source: Getty Images
Mutane 14 sun mutu a hatsarin jirgi
Jami'ai sun riga sun tura ƙungiyar bincike zuwa inda abin ya faru, amma bayanan farko sun nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon rashin kyawun yanayi, in ji rahoton The Sun.
Jirgin, samfurin Cessna 208 Caravan, ya tashi ne daga garin Yei da misalin ƙarfe 9:30 na safe agogon yankin, amma jami'an kula da zirga-zirga sun rasa sadarwa da shi bayan mintuna 30 da tashi.
Takardar shaidar fasinjoji ta nuna cewa mutane 14 ne a cikin jirgin, waɗanda suka haɗa da matuƙin jirgi guda da fasinjoji 13, inda 12 daga cikinsu ƴan Sudan ta Kudu ne yayin da biyu kuma ƴan ƙasar Kenya ne.
Wannan na zuwa ne yayin da wani jirgin sama da ke ɗauke da miliyoyin daloli ya yi hatsari a garin Minga Guazu na ƙasar Paraguay, wanda hakan ya janyo turmutsitsin kwashe kuɗaɗe.
Jirgi dauke da kudi ya yi hatsari
Jirgin ya kasance yana ɗauke da kimanin dala miliyan 5 da kuma miliyoyin kuɗin Brazil (Reais) na wani kamfanin tsaro mai suna Prosegur.
Mazauna yankin sun yi amfani da damar inda suka duƙufa tura damin kuɗaɗen cikin aljihunsu yayin da jirgin ke ci gaba da ƙonewa, cewar rahoto Reuters.
Masu bincike sun bayyana cewa har yanzu akwai kusan dala miliyan 1.3 da kuma Reais miliyan 4 da ake nema waɗanda aka yi awon gaba da su.
Wannan mummunan hatsari ya yi sanadin mutuwar matuƙin jirgin tare da raunata wasu mutane da dama da ke cikinsa.

Source: Getty Images
Kalubalen tsaro a Sudan ta Kudu
Sudan ta Kudu, wadda ita ce ƙasa mafi ƙanƙanta a duniya, tana fuskantar ƙalubale mai girma a fannin sufurin jiragen sama saboda rashin ingantaccen tsari da tsofaffin jirage.
Rahoton BBC ya nuna cewa tun bayan samun ƴancin kai a shekarar 2011, fiye da jirage 55 ne suka yi hatsari a ƙasar, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Yawancin waɗannan hatsuran ana ɗora alhakinsu ne kan cika jirgi da kaya fiye da ƙima, rashin bin dokokin sufuri, da kuma kuskuren matuƙan jirgi.
Jirgin sojoji ya fada kan gidajen mutane
A wani labari, mun ruwaito cewa, an rasa rayukan fararen hula da sojoji da wani jirgin yakin sojin Sudan ya faɗo a kan gidaje a wata unguwa a yankin birnin Khartoum.
Hukumomin kasar Sudan sun tabbatar da cewa mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun samu raunuka daban-daban, suna karɓar magani a asibiti.
Jirgin saman ya gamu da hatsari ne sakamakon tangarɗar na'ura a daidai lokacin da sojojin Sudan ke ci gaba da fafatawa da dakarun kungiyar RSF.
Asali: Legit.ng


