'Har da Ƴata': Shugaban Ƙasa Ya Koka kan Yadda Mazan Najeriya Ke Kwashe Matan Kenya
- Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya koka kan yadda 'ya'yansu mata da dama ke auren maza 'yan Najeriya, ciki har da 'yarsa, June Ruto
- A wani taro, Ruto cikin barkwanci ya ce matan Kenya na komawa zuwa Najeriya, yana tambayar dalilin da ya sa mazansu ba sa samun matan can
- Ruto ya ce yana goyon bayan auren ’yarsa, amma da wuya ya yarda, musamman da ta auri dan kabilar Igbo daga Najeriya a Yammacin Afrika
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nairobi, Kenya - Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya bayyana yadda 'yan matan Kenya ke auren maza 'yan Najeriya, har da 'yarsa ma.
Shugaba Ruto a wani taro ya faɗi haka cikin raha inda ya ke tambayar dalilin faruwar hakan yayin da mazan Kenya ba su samun matan Najeriya.

Asali: Getty Images
Shugaban Kenya, Ruto ya soki mazan kasar
Yayin wata liyafar biki, Ruto ya ce ya lura da yadda matan Kenya ke auren 'yan Najeriya, yana tambayar ko mazan Kenya sun gaza ne, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wani faifan bidiyo, Ruto ya nuna damuwa kan yadda abin ke kara kamari inda ya ce har da ƴarsa a lamarin.
Ruto ya ce ya kamata a nemo hanyar kawo gyara kan abin da ke faruwa saboda ka da a samu ƙarancin mata a kasar Kenya.
Ya kalubalanci mazajen Kenya da cewa anya kuwa suna da kuzari ko jarumta da za su rike matansu a gida.
A cewarsa:
"Yata ta auri dan Najeriya, yanzu kuma wannan ta sake auren dan Najeriya. Mazanmu fa? Ban sani ba, ko kuna da sanyi ne?"
A cikin raha, Ruto ya ce idan haka ya ci gaba, Kenya za ta fuskanci ƙarancin mata saboda suna barin kasar ta hanyar aure.
“Muna bukatar daidaita wannan, saboda idan hakan ya ci gaba, za mu rasa masu hazaka."
- Cewar Ruto

Asali: Facebook
Yar shugaban Kenya ta aure dan Najeriya
June Ruto, 'yar Shugaba Ruto, ta yi aure da wani dan Najeriya mai suna Dr Alexander Ezenegu, a ranar 27 ga Mayun shekarar 2021 wanda yanzu shekaru huɗu kenan.
Duk da goyon bayansa, Ruto ya amince cewa da wuya ya yarda da auren 'yarsa da dan Najeriya tun farko.
Ya ce a wajen bikin, 'Wannan lokaci ne mai dadi da damuwa. Ba sauki ba ne ka ba wani 'yarka saboda akwai jin zafin rabuwa da yara ko babu komai'.
“Ya fi wahala idan wanda za ka ba ’yarka dan Najeriya ne, kuma ya fi wahala idan wanda za ka ba ’yarka dan kabilar Igbo ne."
- In ji Ruto
Shugaban Kenya ya sallami daukacin ministocinsa
Kun ji cewa Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya yi jawabi kai tsaye ga al'ummar kasar bayan da ya rusa majalisar ministocinsa baki daya.
Shugaba Ruto ya kori ministocin ne sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a fadin kasar na tsawon makonni.
Wadanda wannan korar ba ta shafa ba sun hada da sakataren gwamnatin kasar da ministan harkokin wajen kasar, Musalia Mudavadi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng