Yadda Jami'an Tsaro Suka Kubutar da Dalibai 17 daga Hannun Boko Haram
- Jami'an tsaro sun samu nasarar ceto wasu daga cikin daliban jihar Kogi da wasu 'yan ta'adda suka sace a wata gidan marayu
- An kwato dalibai 17 daga cikin wasu dalibai sama 26 da aka sace a gidan marayu wanda ke hade da makaranta a wajen gari
- Har yanzu, akwai sauran dalibai da ke hannun yan ta'addan yayin da ake ci gaba da laluben yaran da aka sace a dazukan jihar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kwara – Jami’an tsaro sun samu nasarar kubutar da dalibai da almajirai guda 17 da aka sace a jihar Kogi bayan yan ta'addan sun kutsa har cikin makarantar, suka yi awon gaba da su.
Sai dai duk da wannan kokari har yanzu wasu mutum tara, da suka hada da mata biyu, na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane.

Source: Getty Images
Zagazola Makama ya wallafa cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an samu wannan nasara ne bayan ci gaba da gudanar da farmaki da bincike da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka yi.
Jami'an tsaro sun ceto dalibai
A rahoton, jami'an tsaro sun bayyana cewa an yi aikin ceto ne biyo bayan rahoton sace mutanen da aka samu a ranar 27 ga watan Afrilu.
A cewar majiyoyin, waɗanda aka ceto sun haɗa da Sultan, Zeidah, Ahmed, Yusuf, Farooq, Museen, Mustapha, Hasheem, Mohammed daToheer.
Sauran wadanda suka samu tsira sun hada da Abdulmumin, Abdulazeem, Mahmud, Ameerah, Firdaus, Tabarakallah da Ibrahim.
An ce an kubutar da su ne bayan da jami’an tsaro suka bi sahun masu garkuwa da mutane ta hanyar amfani da bayanan sirri da kuma kai hare-hare a wuraren da ake zargin maboyarsu.
Akwai sauran dalibai wajen 'yan ta'adda
Sai dai majiyoyin sun ƙara da cewa har yanzu akwai mutum tara da ke tsare a hannun masu garkuwa, daga ciki har da Habibullah, Shakir, Ahmed da Abdulhammed.
Sauran sun hada da Mubarak, Sultannah, Zulaiha, da kuma matan mai makarantar da aka bayyana da suna Nana-Hawa da Halimat.
Jami’an tsaro sun ce sun ƙara kaimi wajen bincike a dazuka da sauran wuraren da ake zargi domin gano inda masu garkuwa da mutanen ke ɓoye, tare da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda ke hannunsu.

Source: Original
Haka kuma an tura jami’ai zuwa muhimman wurare domin tsaurara matakan tsaro, inda ake gudanar da binciken ababen hawa da fasinjoji a manyan hanyoyi, musamman a yankunan Kabba Junction da Zariagi.
Bugu da ƙari, jami’an tsaro na ci gaba da sintiri, tattara bayanan sirri da kuma sanya ido domin hana masu garkuwa da mutane tserewa ko kuma sauya matsuguni.
Majiyoyin sun jaddada cewa ana yin duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa an kubutar da sauran mutanen cikin ƙoshin lafiya, tare da kamo waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika.
An sace wasu dalibai a makaranta
A baya, mun wallafa cewa wasu ‘yan bindiga sun afka wa wani gida a Emohua suka sace dalibai biyar na Jami’ar Rivers, lamarin da ya tayar da hankula a jihar tare da jefa jama'a cikin fargaba.
Hakan na faruwa ne kwanaki bayan dalibai sun koka kan hare-haren kungiyoyin daba tare da neman a mayar da su wani waje na daban domin a kare rayukansu daga barazanar.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tana farautar ‘yan bindigar domin ceto wadanda aka sace da kuma dawo da su wajen yan uwansu lami lafiya.
Asali: Legit.ng


