‘Da Sauran Rina a Kaba’: Trump Ya Fadi Abin da Ya Rage tsakaninsa da Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai gargadin yiwuwar kai sabon hari kan cibiyar nukiliyarta
- Trump ya yi ikirarin cewa Iran za ta dauki sama da shekaru 20 kafin ta farfado daga barnar da aka yi, yana mai cewa Amurka ba ta janye ba
- Rahotanni sun ce Iran ta kara kai hare-hare a Gabas ta Tsakiya, inda Jordan, Kuwait da Bahrain suka fuskanci hare-hare bayan sabuwar rikicin da Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washinton DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa har yanzu kasarsa ba ta kammala da kasar Iran ba.
Trump ya ce bai kammala daukar matakai kan Iran ba, yana mai gargadin cewa wani sabon hari na soja na iya kai wa cibiyar nukiliyar da ake kira tsibirin Pickaxe.

Source: Facebook
Ya yi wannan bayani ne yayin ganawarsa da shugaban Lebanon, Joseph Aoun, a Fadar White House, inda ya ce Iran ba za ta iya dakile shirin Amurka ba, cewar New York Post.
Yadda tsibirin Pickaxe yake a Iran
An ce tsibirin Pickaxe wata cibiyar nukiliya ce da ke karkashin kasa kusa da Natanz, inda hukumomin leken asirin kasashen Yamma ke zargin Iran da gina wata cibiyar tace sinadarin uranium ba tare da bayyana hakan ba.
Trump ya ce za a kai hari mai tsanani kan yankin nan ba da jimawa ba, yana mai cewa duk da ba kasafai yake bayyana wuraren da ake shirin kai hari ba, wannan karon babu abin da Iran za ta iya yi.
Ya ce:
"Za mu kai hari a wannan wurin nan ba da jimawa ba, kuma da zafi sosai.
"Idan muka janye a wannan lokacin, zai ɗauki Iran shekara 20 zuwa 25 kafin ta sake farfaɗowa, to, kuma ba mu gama da ita ba ko kaɗan... ba za mu janye a yanzu ba."

Source: Getty Images
Hasashen da Donald Trump ya yi
Trump ya kuma yi hasashen cewa idan Amurka ta dakatar da hare-haren yanzu, Iran za ta dauki tsakanin shekaru 20 zuwa 25 kafin ta sake gina abin da aka lalata.
A cewarsa, Amurka ba ta da niyyar janyewa daga matakan da take dauka kan Iran a wannan lokaci, yana mai jaddada cewa har yanzu akwai sauran aiki, cewar Punch.
A lokaci guda kuma, rahotanni sun nuna cewa Iran ta kara kaimi wajen kai hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya makonni biyu bayan sake barkewar rikici tsakaninta da Amurka.
An ruwaito cewa kasashen Jordan, Kuwait da Bahrain sun fuskanci hare-hare a ranar Talata yayin da rikicin ke ci gaba da tsananta a yankin.
Martanin Trump da Iran ta kashe sojojinsa
An ji cewa an kashe sojojin Amurka biyu a Jordan yayin da suke kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Iran.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sojojin da hare-haren Iran suka ritsa da su sun mutu ne “a bakin aiki domin kare ƙasarsu”.
Sojojin Amurka 16 sun mutu, yayin da sama da 430 suka jikkata tun bayan fara yaƙin a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.
Asali: Legit.ng


