Wa'azin kasa: Henry ya musulunta, ya koma Musa a Abuja

Wa'azin kasa: Henry ya musulunta, ya koma Musa a Abuja

Labarin da muke samu na nuni ne da cewa a ranakun karshen makon da ya gabata ne na Asabar da Lahadi kungiyar nan ta Jama'atul Izalatul bidi'a wa'ikamatussunna (JIBWIS) watau Izala a takaice bangaren da ke da hedikwatar ta Jos ta gabatar da wa'azin ta na kasa a Abuja a filin 'Eagle Square'.

Haka ma dai mun samu cewa malamai daga sassa daban-daban na fadin kasar nan ne kai har ma da kasashe makwafta suka halarci wa'azin inda aka gudanar da wa'azuzzika da harsuna daban-daban na Najeriya.

Wa'azin kasa: Henry ya musulunta, ya koma Musa a Abuja
Wa'azin kasa: Henry ya musulunta, ya koma Musa a Abuja

KU KARANTA: An kone wani saurayi kan satar Naira dubu 4

Legit.ng ta samu cewa cikin ikon Allah ne ma bayan malamai sun yi wa'azuzka masu ratsa jiki sai ga wani mabiyin addinin kirista yace wa'azin ya ratsa shi, don haka ba abinda yake kauna sa musulunci.

Kamar yadda muka samu haka zalika cewwa a nan take ne ma shugaban taron kuma shugaban majalisar malamai na kungiyar watau Sheikh Sani Yahaya Jingir ya lakana masa kalmar shahada ya sauya sunansa daga Henry zuwa Musa.

A wani labarin kuma, Yayin da kasar Saudiyya ke ta dada kara shiga cikin cakwakiyar rikicin addini sakamakon kokarin kawo sauye-sauye a kasar da Yarima Mohammed bin Salman ke yi, ya bayyana cewa shi a kasar sa yanzu babu sauran banbanci a tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunni.

Yariman yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da wata jaridar Atlantic a nahiyar turai inda yake ziyarar aiki tun satin da ya shude.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng