Duk da Rasa Kujerarsa, Tsohon Minista Ya ba da Mamaki kan Magana game da Tinubu
- Tsohon ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ya yi magana bayan Shugaba Bola Tinubu ya sallame shi daga mukaminsa
- Edun ya nuna godiya ga Bola Ahmed Tinubu bayan cire shi, yana mai bayyana hidimar da ya yi a matsayin abin alfahari gare shi
- Ya ce gwamnatin ta samu tattalin arziki cikin rauni amma ta yi ƙoƙarin daidaita shi, inda ya ce an samu ƙaruwa a lokacinsa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ministan kudi kuma mai kula da tattalin arziki, Wale Edun, ya yi martani ga shugaban kasa bayan rasa kujerarsa ta minista.
Edun ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu duk da cire shi daga mukaminsa inda ya bayyana jin dadi game da ba shi dama da ya yi.

Source: Facebook
Tsohon minista ya yi godiya ga Bola Tinubu
A wata sanarwa da ya fitar wanda Leadership ta samu, Edun ya bayyana cewa hidimar da ya yi a gwamnati gata ce da ya yi alfahari da ita matuka a rayuwarsa.
Har ila yau, Edun ya gode wa shugaban ƙasa bisa amincewar da ya ba shi tun daga farkon mulkinsa har zuwa yanzu da ya bar kan kujerar minista.
Ya tuno cewa ya fara aiki a matsayin shugaban kwamitin sauyin gwamnati, daga bisani ya zama Mai ba shugaban ƙasa shawara kan manufofin kuɗi kafin daga baya aka naɗa shi ministan kudi.
Edun ya ce sun karɓi tattalin arzikin ƙasa cikin mawuyacin hali, amma sun yi aiki tare domin daidaita yanayin tattalin arziki da inganta dorewar kuɗaɗe.
A cewarsa, hakan ya taimaka wajen inganta motsin tattalin arziki daga kusan kashi biyu zuwa sama da kashi huɗu, yayin da hauhawar farashi ta ragu daga kashi 35 zuwa 15.
Ya ce an gudanar da gyare-gyaren ne domin dawo da amincewar jama’a da kuma jawo hankalin masu zuba jari, tare da tabbatar da ci gaban da ya shafi kowa.

Source: Twitter
Edun ya ambaci tsofaffin abokan aikinsa
Edun ya gode wa abokan aikinsa a majalisar zartarwa da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar.
Ya kuma bayyana cewa duk da akwai sauran aiki, yana da kyakkyawar fata cewa an kafa tubalin ci gaba mai ɗorewa ga tattalin arzikin Najeriya.
A ƙarshe, ya yi wa wanda zai gaje shi fatan alheri, yana mai cewa zai ci gaba da bada gudummawa wajen cigaban ƙasa, cewar Vanguard.
Ministan da Tinubu ya kora ya yi martani
Mun rahoto muku cewa tsohon ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa, ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi a gwamnatinsa.
Dangiwa ya bayyana cewa ya yi amfani da lokacinsa a matsayin minista wajen bayar da gudunmawar tabbatar da nasarar "Renewed Hope Agenda".
Yayin da yake shirin miƙa ragama, tsohon ministan ya lissafa wasu daga cikin manyan nasarorin da ya samu a shekarun da ya yi kan kujerar daga Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

