Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

Tun a watan Disambar shekarar 2019 ne aka fara samun bullar annobar cuta mai toshe numfashi ta Coronavirus a kasar China, inda daga nan ta watsu zuwa kasashe 151, daga ciki har da Najeriya.

Ita dai wannan cuta a yanzu haka ta kama sama da mutane 200,000 a duniya, tare da kashe akalla mutum 1000, kuma babban tashin hankalin shi ne har yanzu babu tabbacin takamaimen maganinta.

KU KARANTA: Yan Najeriya biyu, mai jego da jaririnta sun kamu da cutar Coronavirus

Bullar wannan cuta ta haifar da matsaloli da dama ga kasashen duniya, musamman ta bangaren tattalin arziki, inda ta sabbaba karyewar farashin gangan danyen mai a kasuwar duniya, tare da hana jama’a walwala wanda hakan tasa gwamnatoci a duk fadin duniya daukan tsauraran matakan hana yaduwarta.

A nan gida Najeriya ma an samu bullar cutar a jikin mutane 8, don haka gwamnatocin jahohi suka bi sawun gwamnatin tarayya wajen kare yaduwar cutar ta hanyar garkame makarantu da kuma hana duk wasu taruka masu tara jama’a.

Ga wasu daga cikin jahohin:

- Jahar Kaduna za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Katsina za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Kano za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Jigawa za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Kebbi za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Zamfara za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Sakkwato za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Neja za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Kwara za ta kulle makarantu daga ranar Litinin 23 ga watan Maris

- Jahar Legas ta kulle makarantu, ta hana sallar jama’a, ta hana bautan Coci da tarukan jama’a

- Jahar Enugu za ta kulle makarantu daga ranar Juma’a 27 ga watan Maris

- Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta za ta rufe makarantu daga ranar Juma’a 20 ga watan Maris

- Jahar Ogun ta hana taron kallo fina finai a Silima, bude gidajen abainci, kallon wasannin motsa jiki dss

Ita ma majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da zaman majalisa har sai yadda hali yayi, haka zalika kungiyar addinin Musulunci ta Ansaruddeen ta dakatar da sallar Juma’a a masallatanta gaba daya.

Ita ma kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN ta umarci a garkame coci coci don hana jama’a cudanya, shi ma shehin Malami Dahiru Bauchi ya ce za’a iya daina yin musabaha saboda wannan cuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel