Bukola Saraki Ya Fadi yadda Buhari Ya Gallaza Masa da Ya ke Shugaban Majalisa
- Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce Muhammadu Buhari ya gallaza masa saboda ya soki yawan cin bashi da ya yi
- Saraki ya ce shiru da rashin goyon bayan da ya samu daga ‘yan Najeriya ne ya haddasa raunin majalisun da suka biyo bayansa
- Ya kuma zargi masu mulki da rashin shiri mai kyau wajen shirya wa tafiyar da gwamnati da kuma guje wa masu basira a cikin siyasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya zargi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gallaza masa saboda ya yi tir da yadda ya ke cin bashi ba tare da tsari ba.
Saraki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron tsofaffin ɗaliban King's College (KCOBA) na Arewacin Amurka da aka gudanar a Houston, Texas.

Asali: Facebook
Wani rahoto da tashar Arise News ta wallafa ya nuna cewa an karrama Bukola Saraki da lambar yabo yayin taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saraki ya ce rashin goyon bayan manyan ‘yan ƙasa da talakawa a lokacin da yake fuskantar matsin lamba ya sa shugabanin majalisa da suka biyo bayansa zama 'yan amshin shata.
Saraki: 'Buhari ya gallazawa majalisa a lokacina'
Saraki ya bayyana cewa majalisar dattawa da ya shugabanta daga 2015 zuwa 2019 ta sha matsin lamba daga gwamnatin Buhari.
Ya ce an shigo da ƙorafe-ƙorafe na ƙarya da shari’o’i da suka shafi dukiyarsa lokacin yana gwamna a Kwara.
This Day ta rahoto cewa Saraki ya ce:
“An yi wa majalisa katsalandan a lokacina, an tsorata ta, kuma an hana ta yin da dokokin da za su amfanar da jama’a. Sai dai babu wanda ya tsaya ya kare mu – ba manya ba ƙanana.”
Saraki ya ce saboda irin haka shugabannin majalisa da suka zo bayansa kamar Ahmad Lawan da Godswill Akpabio suka zama 'yan amshin shata, domin gudun a maimaita abin da ya same shi.
Saraki ya soki sakacin ‘yan siyasar Najeriya
Bukola Saraki ya kuma zargi shugabannin siyasa da rashin shiri da ƙwarewa wajen tafiyar da gwamnati.
Ya yi magana yana mai cewa yawanci daga cikinsu ba su da tsare-tsare ko manufofi na ci gaba sai dai bin son rai ko shawarwarin ‘yan shan miya da ke kewaye da gwamnati.
Bukola Saraki ya ce:
“Matsalar Najeriya ba ta shugabanni kaɗai ba ne, har da ‘yan ƙasa da suka gaza tsayawa da gaskiya wajen zaɓen nagartattun shugabanni.
Har yau, waɗanda suka fi dacewa da mulki ba sa shiga siyasa.”
Saraki ya yi kira ga masu ilimi da kwarewa da su daina ɓoye kai, su shiga siyasa ko su tallafa wa nagartattun ‘yan takara da kuɗi da muryoyinsu.

Asali: Twitter
Saraki zai jagoranci kwamitin sulhun PDP
A wani rahoton, kun ji cewa PDP ta yi wani taro na musamman a birnin tarayya Abuja domin warware matsalolinta.
An zabi tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya jagoranci kwamitin sulhu.
Ana sa ran Bukola Saraki zai tattauna da 'yan kwamitin da zai yi aiki tare da su domin kawo mafita wa PDP kafin zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng