Dangote Ya Yi Gogayya da Trump a Jerin Mutane 100 Mafi Tasiri a Duniya
- An fitar da jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya a shekarar 2026, inda hamshakin dan kasuwa a Najeriya, Aliko Dangote ya shiga cikinsu
- Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Amurka, Donald Trump na cikin wadanda suka haska a jerin mutanen da aka fitar a wannan shekarar
- Legit Hausa ta gano cewa mutanen da aka zaba sun hada da shugabanni, 'yan kasuwa, masana kimiyya da fasahar zamani da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hamshakin attajirin Najeriya, Aliko Dangote da Shugaban Amurka Donald Trump sun shiga cikin jerin mutane 100 mafi tasiri na mujallar TIME na shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa hakan ya tabbatar da ci gaba da fitowar tasirinsu a kasuwannin duniya, manufofi da tsarin shugabanci a yau.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya kira Sarkin Qatar ta wayar tarho, an ji maganar da suka yi kan Iran

Source: Getty Images
Dangote ya shiga cikin manyan duniya
Mujallar Times ta fitar da jerin a ranar 15 ga Afrilun 2026, inda ta girmama mutanen da ke tsara makomar duniya a fannoni kamar kasuwanci, siyasa, fasaha da al’adu.
Dangote, Donald Trump sun kasance tare da manyan mutane irin su Xi Jinping, Mark Carney da Fafaroma Leo XIV, da kuma masana fasaha kamar Sundar Pichai da Neal Mohan cikin masu tasiri a duniyar yau.
Dangote, wanda aka saka a rukunin “Titans”, shi ne dan Najeriya daya tilo a jerin na 2026, duk da cewa ba shi kadai ba ne daga Afirka.
Sauran ‘yan Afirka da aka karrama sun hada da Netumbo Nandi-Ndaitwah, Precious Matsoso, Anok Yai, Mamadou Amadou Ly da Zabib Musa Loro.
Wannan shi ne karo na biyu da Dangote ke shiga jerin mutane 100 da ake fitarwa, bayan an taba karrama shi a 2014 saboda tasirinsa a kasuwanci da ayyukan jin kai.
Masana na ganin cewa komawar Dangote cikin jerin mutane masu tasiri bayan fiye da shekaru 10 na nuna yadda tasirinsa ya dore kuma ya karu.
Nasarorin da Dangote ya samu
A matsayin wanda ya kafa manyan masana’antu a Afirka, Dangote ya zuba jari a fannoni da dama kamar hada siminti, sukari, samar da taki, noma da gina abubuwan more rayuwa, tare da fadada zuwa bangaren makamashi.
Punch ta wallafa cewa an ce wadannan kamfanoni da Dangote ya kafa sun taimaka wajen rage dogaro da kayayyakin waje, samar da ayyukan yi.

Source: Facebook
Sauran mutanen da aka karrama a duniya
Sauran manyan da aka karrama tare da Aliko Dangote sun hada da Reid Wiseman, Michael Dell da Susan Dell, da Ralph Lauren.
A rukunin “Pioneers”, an karrama mutane da suka kawo gagarumin cigaba a kimiyya da cigaban al’umma kamar Kiran Musunuru, Rebecca Ahrens-Nicklas da Aaron Williams.
Jerin ya kuma hada da fitattun mutane a harkar nishadi da al’adu kamar Ranbir Kapoor, Dakota Johnson, Kate Hudson da sauransu.
Dangote ya rage kudin mai

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote da ke Legas ta yi rangwame game da farashin man fetur yayin da 'yan Najeriya ke korafi.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa matatar Dangote ta rage N75 da ta kara a baya a sabon farashin man fetur da ta fitar.
Ana cigaba da fuskantar matsalar man fetur ne biyo bayan tashin farashin danyen mai saboda yakin da Amurka da Iran ke yi a Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng
