Sarki Sanusi II Ya Isa Kasar Tunusia Babban Taron Tattali na Afrika na 2025

Sarki Sanusi II Ya Isa Kasar Tunusia Babban Taron Tattali na Afrika na 2025

  • Khalifa Muhammad Sanusi II, ya isa kasar Tunisia domin halartar babban taron zuba jari da ciniki na Afrika (FITA2025)
  • Taron za su gudana ne daga ranakun 6 zuwa 7 ga watan Mayu, 2025, a babban otal din Radisson Blu da ke birnin Tunis
  • Sarkin ya samu rakiyar manyan masu sarauta daga Kano, ciki har da Sarkin Shanun Kano, Nazir Halliru da Jarman Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tunusia - Mai martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, ya isa kasar Tunisia domin halartar babban taron kasa da kasa na zuba jari da ciniki a nahiyar Afrika, wanda ake kira FITA2025.

Ana fatan ziyarar za ta taimaka wajen gano sababbin hanyoyin jawo zuba jari da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano da Najeriya baki daya.

Sanusi II
Sarki Sanusi ya isa Tunusia halartar taron tattali na Afrika. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Tawagar Muhammadu Sanusi II a Tunisia

Legit ta gano bayanai kan ziyarar da Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kai Tunusia ne a cikin wani sako da masarautar Kano ta wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya samu rakiyar wasu manyan masu rike da sarautar gargajiya daga masarautar Kano, wadanda suka hada da Nazir Halliru, Sarkin Shanun Kano, da kuma Jarman Kano.

Taron zai gudana ne daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Mayu, 2025, a babban otal din Radisson Blu da ke birnin Tunis.

An shirya taron ne a karkashin kungiyar Tunisia Africa Business Council (TABC), wanda ke bikin cika shekaru 10 da kafuwa, tare da gudanar da zagayen taron karo na takwas.

Manufar taron da Sanusi II ya halarta a Tunis

Shafin Africa CEO ya wallafa cewa babban manufar taron ita ce samar da sababbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen Afrika.

Baya ga haka, taron zai samar da wani dandalin haduwa tsakanin masu ruwa da tsaki daga kasashen duniya.

FITA2025 zai bai wa mahalarta damar halartar tarurruka na musamman, tattaunawa, da tarukan kwararru da za su tabo batutuwan da suka shafi farfado da tattalin arzikin nahiyar Afrika.

Har ila yau, taron zai karfafa cinikayya tsakanin kasashen Afrika da janyo masu zuba jari daga kasashen waje.

Ana sa ran manyan wakilan gwamnatoci, cibiyoyin kasashe da na duniya, masu zuba jari, da shugabannin kamfanoni za su halarci taron domin duba hanyoyin tallafa wa tattalin Afrika.

Sanusi II
Ana sa ran Sanusi II zai tallata Najeriya wajen taron tattali a Tunusia. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Tsammani da ake yi wa Sanusi II a taron

A matsayinsa na masanin tattali, ana ganin ziyarar Sarki Sanusi II na cikin kokarinsa na neman sababbin damammaki na jari da ci gaba ga jihar Kano da Najeriya baki daya.

Ana cewa Sanusi II da ya shahara wajen fadin albarkacin baki kan batutuwan tattali da shugabanci zai yi amfani da dandalin domin janyo hankalin masu zuba jari Kano da Najeriya.

A yanzu haka dai an zuba ido domin ganin rawar da Sanusi II zai taka wajen tallata Najeriya a wajen taron.

Sanusi II ya ziyarci kasar Burkina Faso

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ziyarci kasar Burkina Faso.

Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Burkina Faso ne domin halartar nadin sabon Khalifan Tijjaniya na kasar.

Bayan nadin sabon Khalifan Darikar, Muhammadu Sanusi II ya gana da shugabannin kasar da sauran masu ruwa da tsaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng