Pantami Ya Yi Maganar Siyasa, Ya Haska Dalilin da Zai Sa a Zabe Shi a 2027
- Tsohon Ministan sadawa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya halarci taron baje kolin ayyukan da ya gudanar lokacin da yake cikin gwamnati
- Farfesa Pantami ya alakanta ayyukan da ya gudanar da batun neman kuri'un jama'a a zaben shekarar 2027
- Malaman addinin Musulunci ya bayyana cewa ayyukan da ya gudanar sun karade kowace jiha a cikin tarayyar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi magana kan ayyukan da ya gudanar a baya.
Farfesa Pantami ya bayyana cewa ayyukan da ya gudanar a lokacin da yake kan muƙamin gwamnati su ne za su ba da shaidar cancantarsa gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa tsohon Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taro na baje kolin ayyuka da shirye-shiryen da ya aiwatar lokacin yana Miinista, a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.
Ana rade-radin cewa tsohon Ministan yana zawarcin kujerar gwamnan jihar Gombe a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.
Wadanne ayyuka Isa Pantami ya gudanar?
Yayin taron, Farfesa Pantami ya bayyana cewa ya aiwatar da dubban tsare-tsare a faɗin Najeriya cikin shekaru huɗu.
Tsohon ministan ya bayyana cewa yawancin waɗannan tsare-tsare sun mayar da hankali ne kan sauye-sauyen fasahar zamani, tallafa wa matasa, da haɓaka tattalin arziƙi.
Ya jaddada cewa ayyukan nasa sun bazu a duk faɗin tarayyar ƙasar nan domin tabbatar da adalci da tasiri ga ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa babu wata jiha da aka ware da gangan, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Farfesa Pantami, wanda ya taɓa zama shugaban hukumar NITDA daga 2016 zuwa 2019, sannan Minista daga 2019 zuwa 2023, ya ce bayanan ayyukan da ya yi suna nan a buɗe domin kowa ya duba.

Source: Facebook
Pantami ya ce ba a zarginsa da rashawa
'Dan syasar ya jaddada cewa duk da shekarun da ya yi a gwamnati, babu wata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta taɓa gayyatarsa ko tuhumarsa da wani laifi.
“Ba zan je wurin mutane da alkawuran fatar baki ba, zan je musu ne da sakamakon ayyukan da na riga na yi. Idan kana son gabatar da kanka don kowane muƙami, ka zo da sakamakon ayyukanka ka nuna cewa an gwada ka kuma an amince da kai."
- Farfesa Isa Ali Pantami
Sheikh Pantami ya ki amsa tayin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce yana da kyakkyawa alaka da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Pantami ya bayyana cewa mutane da dama ba su san irin rawar da ya taka ba wajen nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2023.
Malamin ya ce Tinubu ya yi masa tayin mukamai har guda uku, amma ya ki karba, ya sanar da shi cewa zai mayar da hankali ne kan wasu abubuwa da ya sanya a gabansa.
Asali: Legit.ng

