Shari'ar Sambo Dasuki, Babbar Kotu a Abuja Ta Watsawa Hukumar DSS Kasa a Ido

Shari'ar Sambo Dasuki, Babbar Kotu a Abuja Ta Watsawa Hukumar DSS Kasa a Ido

  • Babbar kotu a Abuja ta yi watsi da bukatar DSS ta sake gabatar da wasu hujjoji da ta taba mikawa a shari’ar Sambo Dasuki
  • Mai shari’a Peter Lifu ya ce sake karɓar irin waɗannan hujjoji zai zama “rashawa ta shari’a da raina hankalin kotu.”
  • Lauyan Sambo Dasuki ya ce DSS na son yin abin da ya saba doka, domin kotu ba za ta saurari hujjojin da ya yi watsi da su ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta watsa wa hukumar DSS kasa a ido, a shari'arta da Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya).

Alkali dai ya ƙi amincewa da bukatar DSS na sake gabatar da hujjoji da kotun ta taɓa ƙin karɓa a shari’ar tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro.

Kara karanta wannan

Bakary: Dan adawar Kamaru ya ce ya kayar da Paul Biya a zaben shugaban kasa

Kotu ta ki amincewa da bukatar DSS a shari'ar Sambo Dasuki
Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsari, Sambo Dasuki a cikin kotu. Hoto: @ronuspirit/X
Source: Twitter

Sambo Dasuki: Kotu ta kunyata hukumar DSS

Mai shari’a Peter Lifu, wanda ya jagoranci zaman kotun a ranar Talata, ya ce ba zai sake sauraron irin hujjojin da kotu ta taɓa ƙin karɓa ba, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun ya bayyana cewa bukatar da hukumar DSS ta gabatar ta yi kama da “rashin mutunta shari’a da kuma rashin lissafi.”

Ita dai wannan shari'ar, ta ta'allaka ne a kan tuhumar da ake yi wa tsohon NSA, Sambo Dasuki na mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

“Kotu ta yi watsi da bukatar” – Alkali

Mai shari’a Lifu ya tuna cewa a ranar 10 ga Yuli, 2025, ya taɓa yanke hukunci na ƙin karɓar hujjojin da DSS ta gabatar saboda ba su da tushe da kuma rashin dacewa da tuhumar da ake yi wa Dasuki.

“Wannan hukunci har yanzu yana nan, kuma ni a matsayina na alkali, zan zauna daram a kansa. Duk wani yunƙuri na canza hukuncin zai zama rashin mutunci ga kotu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda ana batun sulhu a Katsina, mutum 12 sun kwanta dama

"Ko mutum ya ki Allah, ya san babu dalilin sake karɓar irin waɗannan hujjoji. Don haka, wannan kotu ta yi watsi da bukatar gaba ɗaya."

- Mai shari’a Peter Lifu.

Babbar kotun tarayya ta ce raina kotu ne a yi watsi da hujjoji kuma a sake dawo da su.
Ginin babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: David Exodus/Bloomberg
Source: Getty Images

Lauyan DSS ya nemi a sake duba hujjojin

A zaman baya na ranar 25 ga Satumba, 2025, lauyan DSS, Oladipupo Okpeseyi (SAN), ya nemi kotu ta je ofishin DSS domin duba motocin da aka ce an kwace daga gidan Dasuki, wadanda aka ajiye tun shekara ta 2015.

Ya ce hukumar ta gyara kura-kuran da suka jawo ƙin karɓar hujjojin a baya, don haka ya nemi a sake karɓar su, inji rahoton Punch.

Sai dai lauya mai kare Dasuki, A. A. Usman, ya bayyana wannan bukata a matsayin “abin ban mamaki da doka ba ta yarda da shi ba.”

“Da zarar an ƙi amincewa da shaida a kotu, to ta tsaya a haka kenan. Ba za a sake gabatar da ita ba,” in ji A. A. Usman.

Mai shari’a Lifu ya amince da hujjar lauyan Dasuki, yana mai cewa duk hujjojin da aka ƙi karɓa suna nan a matsayin hujjoji da aka ƙi su gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

An fara kiran a saki Abba Kyari bayan afuwar da Tinubu ya yi wa mutane 175

EFCC ta sake dauko shari'ar Dasuki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC za ta sake gurfanar da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Sambo Dasuki a gaban kotu.

Hukumar, mai yaki da cin hanci da rashawar za ta gurfanar da Dasuki ne da tsohon shugaban NNPCL, Aminu Baba-Kusa, tare da kamfanoni biyu.

Bayanai sun nuna cewa Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) ya na fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi zargin karkatar da kuɗin da suka kai N33.2bn.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com