Kotu Ta Bada Umarni a Karbe Miliyoyi da Gidajen Hadiman Sambo Dasuki Har Abada

Kotu Ta Bada Umarni a Karbe Miliyoyi da Gidajen Hadiman Sambo Dasuki Har Abada

  • Wata Babban kotun tarayya da ke Abuja ta ba EFCC damar karbe miliyoyin kudi da kadarori
  • Hukumar EFCC tace tayi nasara a shari’ar da take yi da Jonah Otunla da Kanal Bello Fadile a kotu
  • Alkali ya bada umarnin a karbe N775m da wasu gidaje da otel da wadannan mutane suka mallaka

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja, ta amince a karbe kudi har N775m da wasu kadarorin Jonah Otunla da Kanal Bello Fadile.

Daily Trust ta kawo rahoto a farkon makon nan cewa hukumar EFCC tayi nasara a kan tsohon Akanta Janar na kasa da hadimin Sambo Dasauki.

Kanal Fadile mai ritaya ya yi aiki da Kanal Sambo Dasauki mai ritaya a lokacin yana rike da ofishin Mai shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro.

Kara karanta wannan

Gwmnati Tana Sa Ido da Kyau, EFCC Tana Bibiyar Kudin da ‘Yan Takara Suke Kashewa

An karbe kudi da gidaje

Kamar yadda jawabin da EFCC ta fitar ya nuna, dukiyar da aka karbe daga hannun wadannan mutane sun hada da wani gida da ke Asokoro a Abuja.

Har ila yau, Alkali ya amincewa jami’an hukumar EFCC karbe wani fuloti da ke Maitama a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga cikin sauran dukiyoyin da aka karbe har abada akwai wani otel da ake ginawa da kuma wani katafaren gida duk a Gwarimpa a babban birnin tarayya.

Kotu.
Wani Kotun Tarayya a Abuja Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Kakakin EFCC na kasa, Wilson Uwujaren yace ana zargin an mallaki wadannan dukiyoyi ne wajen aika-aikar Otunla da Fadile sa'ilin suna da mukami.

Jaridar Tribune ta rahoto Uwujaren yana cewa Otunla da Marigayi Otunba Ade Adelakun sun dawo da N775m da kotu ta bada umarni su dawo da shi.

EFCC tace tana zargin an wawuri wadannan miliyoyi ne daga ofishin NSA a lokacin gwamnatin baya. Dasuki ya rike kujerar NSA lokacin Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai

Alkali ya ba EFCC gaskiya

Alkalin da ya saurari karar, Mai shari’a Donatus Okorowo ya gamsu da hujjojin da masu shigar da kara suka gabatar, sai ya amince da bukatar lauyoyinsu.

Donatus Okorowo ya zartar da hukunci cewa a maida dukiyoyin hannun gwamnatin tarayya.

Da farko kotu tace a rike wadannan dukiyoyi na wucin-gadi, bayan shekaru fiye da biyu ana shari’a a kotu, Alkali ya raba wadanda ake tuhuma da dukiyoyin.

2023 da matsalar tsaro

An samu labari wani babban jami’in ‘dan sanda yace alamu na nuna za a iya fuskantar barazanar rashin tsaro a zaben 2023 musamman a wasu Jihohi.

Tsoron da ake yi shi ne a Borno, za a iya muzgunawa ‘yan takaran jam’iyyun hamayya a zaben badi, sannan kuma rikicin PDP zai iya yin tasiri a Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel