Kudin makamai: Kotu za ta fara zaman hukunta Sambo Dasuki da sauransu

Kudin makamai: Kotu za ta fara zaman hukunta Sambo Dasuki da sauransu

Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Hussein Baba-Yusuf, ya sanya ranar 11 ga watan Mayu a matsayin ranar zama n fara shari’an tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Sambo Dasuki da Bashir Yuguda kan zargin wawure naira biliyan 19.4 na siyan makamai.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta maka Dasuki, Yuguda tare da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa a gaban kotu.

Hakazalika an maka har da dan Bafarawa mai suna Sagir, da kuma wani kamfani maisuna Dalhatu Investment Limited.

Ana tuhumar su da laifuka 25 wadanda suka danganci cin amana, facaka da kudi kimanin naira biliyan 19.4.

Kudin makamai: Kotu za ta fara zaman hukunta Sambo Dasuki da sauransu
Kudin makamai: Kotu za ta fara zaman hukunta Sambo Dasuki da sauransu
Asali: Depositphotos

An dage karar ne saboda lauyan Bafarawa mai suna Lateef Fagbemi ya shaida wa kotu cewa babban lauyan Dasuki bai samu halartar zaman kotun ba, saboda mutuwar matar dansa.

KU KARANTA KUMA: Za a sake shiga matsin tattalin arziki a Najeriya nan ba da jimawa ba - Gwamna Yari

Bayan alkalin ya tabbatar da rasuwar matar, sai ya sa bangaren lauyoyin biyu suka zauna, su ma suka tabbatar da rasuwar ta.

Daga nan ne ya aza ranar 11 ga watan Mayu, domin a ci gaba da shari’a. Tun bayan kama Dasuki a cikin 2015, har yau ba a sake shi ba, ya na tsare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng