Sabon Rikici: Kuwait Ta kai Farmaki kan Jirgin Iran, Tehran Ta Yi Martani
- Yayin da ake zaman tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya zargi Kuwait da kai masu hari
- Araghchi ya bayyana cewa an kai hari ne kan jirgin ruwan Iran tare da kama wasu 'yan kasar da ke tafiya a kan teku ba bisa kai'da ba
- Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka ya ziyarci kasar China, inda ya ce zai yi doguwar tattaunawa game da Iran da Gabas Ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rahotanni sun nuna cewa kasar Iran ta zargi Kuwait da kai haramtaccen hari kan jirgin ruwan ta tare da tsare ’yan ƙasarta.
A martanin da ta yi bayan bayan lamarin, Iran ta buƙaci Kuwait ta saki ’yan ƙasarta huɗu da aka tsare nan take tare da gargadin za ta yi ramako.

Source: Getty Images
Legit ta tattaro bayanai game da zargin ne a wani sako da Mnistan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na X.
An ce Kuwait ta kai hari Iran
Wani sabon rikicin diflomasiyya ya ɓarke tsakanin Iran da Kuwait bayan Tehran ta zargi hukumomin Kuwait da kai hari ba bisa ƙa’ida ba kan wani jirgin ruwa na Iran tare da tsare ’yan ƙasar Iran huɗu.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi zargin cewa lamarin wani yunƙuri ne na ƙara tayar da rikici a yankin.
“A wani yunƙurin haddasa rikici, Kuwait ta kai hari ba bisa ƙa’ida ba kan wani jirgin ruwan Iran tare da tsare ’yan ƙasarmu huɗu a Tekun Farisa,”
In ji Araghchi.
Ministan ya kara da cewa:
“Wannan haramtaccen aiki ya faru ne kusa da wani tsibiri da Amurka ta yi amfani da shi wajen kai hari kan Iran. Muna buƙatar a saki ’yan ƙasarmu nan take kuma mun yi tanadin mayar da martani,”
Mutanen kasar Iran da aka tsare
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana tun da farko cewa mutanen da aka tsare suna da alaƙa da dakarun IRGC
An ce Iran ta kara da cewa suna gudanar da sintiri a teku ne lokacin da matsalar na’urar kewayawa ta sa suka shiga ruwan yankin Kuwait.

Source: Getty Images
Ma’aikatar harkokin wajen ta kuma yi watsi da zargin Kuwait cewa Tehran na shirin aiwatar da ayyukan ta’addanci kan ƙasar.
Rikicin ya biyo bayan zargin da Kuwait ta yi wa Iran ranar Talata cewa ta tura wata ƙungiya mai ɗauke da makamai mai alaƙa da dakarun RIRGC zuwa wani tsibiri da ke ɗauke da tashar jiragen ruwa da China ta ɗauki nauyin ginawa.
Donald Trump ya ziyarci kasar China
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya isa zuwa kasar China a wata ziyarar kwana biyu da ya shirya.
Trump ya bayyana cewa zai yi doguwar tattauna da shugaban China game da Iran da matsalolin da suka addabi Gabas ta Tsakiya.
Hakan na zuwa ne bayan shafe kwana 40 ana gwabza yaki tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila kafin Pakistan ta jagoranci tsagaita wuta.
Asali: Legit.ng


