Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja

Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja

  • Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bada umarnin kwace kadarar 'dan Sambo Dasuki mai daraja N90 miliyan a Abuja
  • Hukumar EFCC ta mika bukatar kwace kadarar wacce gida ne mai dakuna bakwai, bene da dakunan hadimai biyu
  • Kamar yadda EFCC ta bayyana, ta samu bayanan sirri daga ofishin NSA cewa an waskar da wasu kudade lokacin Dasuki na ofishin

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba ta bada umanin kwace kadarar N90 biliyan na wucin-gadi mallakin Abubakar Dasuki, 'dan tsohon mai bada shawara kan tsaron kasa, Sambo Dasuki.

Mai Shari'a Emeka Nwite, a hukuncinsa, ya bada umarnin bayan lauyan EFCC, Olanrewaju Adeola, ya mika wannan bukatar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

Daga nan Mai shari'a Nwite, ya umarci EFCC da ta bada sanarwar kwanaki 14 a jarida da kuma shafinta na yanar gizo idan akwai wani ko wasu da za su iya bada dalilin da zai hana a kwace kadarar ga gwamnatin tarayya tare da dage sauraron shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Yuli.

Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja
Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja. Horo daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kadarar gida ce mai dakunan barci bakwai tare da bene da kuma dakin hadimai biyu, yana nan a lamba D1064 rukunin gidaje na Brains and Hammers, APO, Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karar da Chidi Nwek, SP a EFCC, hukuma a wani lokaci a watan Nuwamban 2015, ta samu rahoton sirri daga ofishin NSA inda aka zaga cewa an biya wasu makuden kudade ga wasu mutane da kamfanoni ta hannun tsohon NSA, Kanal Sambo Dasuki.

Hukumar ta zargi cewa, kudaden an biya su ne daga asusun bankin ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa tsakanin 2012 zuwa 2015 na wasu kwangiloli da ba a bayyana wadanda suka amfana da su ba.

Kara karanta wannan

PDP ta ragu: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour

Sashen bincke na musamman aka umarta domin ya bankado me ke faruwa tare da gano sahihancin rahoton sirrin.

Binciken ya bayyana cewa, daga ckin kudaden da aka biya mutane da kamfanoni an gano cewa an biya Brains an Hammers Ltd N90 miliyan.

Hukumar ta ce an aike wasikar bincike ga wanda ake zargi, bankin, CAC da Brains and Hammes Ltd kuma sun samu martani.

Hukumar EFCC ta ce a yayin binciken, an samo takardun gidan dauke da sunan abubakar Atiku Dasuki. Ta roki kotun da ta saukake lamurran domin adalci ya tabbata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel