Allah Sarki: Yan Bindiga Sun Kai Hari, Sun Hallaka Basarake da Wasu Mutum 2
- Wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kashe dagacin Ukohol da wasu biyu yayin da suke gona a Guma a jihar Benue
- Wani yaro ya tsira da raunuka, yayin da wasu mutane biyu suka bace bayan harin da aka kai musu a gonarsu
- Limamin Katolika ya bayyana bakin ciki kan kisan Zaki Isho da ya kira ɗaya daga cikin manoman da suka fi himma a yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kai farmaki a kauyen Ukohol da ke Guma a jihar Benue.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kashe dagacin kauyen, Zaki Aondohemba Isho, da wasu mutane biyu.

Asali: Facebook
Yan bindiga sun kashe manoma a gonarsu
Wannan mummunan hari ya sake faruwa kasa da makonni uku bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe fiye da mutane 200 a kusa da Yelewata, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda aka kashe akwai tsohon malamin makaranta, Mista Uger Sember, sai wani mutum da ya samu raunuka mai tsanani.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, wadanda aka kashe sun je gonarsu su yi noma ne lokacin da makiyayan suka zo suka bude musu wuta.
Ya ce bayan kisan, yan bindiga sun kona babur din Zaki sannan suka gudu, yayin da wani yaro da ya raka su ya tsira da raunuka.
An tabbatar da cewa yaron yanzu haka yana karbar magani a wani asibiti da ke Daudu domin ceto ƙoƙarin ceto rayuwarsa.
Benue: Fasto ya yi jimamin kisan basaraken
Wani limamin Katolika, Mfa Tivdoo, wanda ya san marigayin, ya bayyana bakin cikinsa a shafinsa na sada zumunta bisa kisan da aka yi masa.
Ya ce marigayin ya kasance ɗaya daga cikin manoman da suka fi aiki tukuru a yankin, kuma ya gan shi sati ɗaya da ya gabata.
Ya ce:
"Ya zo ya same ni a gona yana cewa zai dawo ziyara, sai dai wannan ziyara ba za ta ƙara faruwa ba."

Asali: Original
Halin da ake ciki bayan harin yan bindiga
Har yanzu dai jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba, domin kokarin jin ta bakin jakin rundunar, DSP Udeme Edet bai yi nasara ba.
Al’ummar yankin sun shiga firgici da bakin ciki saboda wannan harin, suna rokon gwamnati ta kawo musu dauki cikin gaggawa.
Harin yana ci gaba da nuna irin matsin da al’ummomin yankin ke fuskanta daga makiyaya masu dauke da makamai.
Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban PDP
A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Miyagun ƴan bindigan sun kai farmakin ne kan shugaban shugaban na PDP a ƙaramar hukumar Tarka a daren ranar Juma'a 20 ga watan Yunin 2025.
Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ta fara farautar wanda ake zargi da kitsa kai harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng