Yan Bindiga Sun Tare Matasa da Ke Dawowa daga Jana'iza, Hadimin Gwamna Ya Tsira

Yan Bindiga Sun Tare Matasa da Ke Dawowa daga Jana'iza, Hadimin Gwamna Ya Tsira

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu masu makoki a kauyen Rim, jihar Plateau, inda suka harbi matashi kuma suka yanke hannunsa
  • Timothy Dantong, jami'in gwamnatin jihar, ya ce harin ya faru ne bayan kammala jana’iza a Bachit, yayin da tankin yaki ya zo ya ceci su
  • Hakan ya biyo bayan kai hari gidan tsohon Minista, Damishi Sango inda aka kashe mace guda kuma wasu uku suka jikkata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Plateau - Wasu 'yan bindiga sun kai hari a ranar Laraba kan wasu masu makoki a kauyen Rim da ke jihar Plateau, inda suka yanke hannun matashi.

An gano cewa masu makokin na dawowa ne daga jana'iza a kauyen Bachit lokacin da 'yan bindigar suka tare su a hanya suka harbi mutum daya.

Yan bindiga sun kai hari kan masu jana'iza a Plateau
Yan bindiga sun farmaki matasa da ke dawowa daga jana'iza. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun farmaki matasa a Plateau

Jami'in hulda da jama'a na Gwamna Caleb Mutfwang a mazabar Riyom, Timothy Dantong, wanda ya tsira daga harin, ya tabbatar da faruwar lamarin, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tankin yaki daga jami’an tsaro ya iso daga baya, inda ya kubutar da shi da sauran mutanen da suka makale a wurin.

Dantong ya ce:

“Jiya na je jana’iza a garinmu Bachit. Yayin dawowa, an kai hari a Rim kuma aka ce mu tsaya kafin mu wuce.
“Mun tsaya fiye da sa’o’i biyar, amma wasu da suka nace sun ci gaba da tafiya sai 'yan bindigar Fulani suka harbe su a hanya.
“Wani matashi aka harba aka kuma yanke hannunsa. Daga baya ne tankin yaki ya iso ya cece mu daga inda muka makale.
“Har da safiyar Alhamis, 'yan bindigar sun sake fitowa suka tare hanyar Wereng suka kai hari kan wasu matafiya da ke babur.

“Ban san me wadannan ‘yan bindigar Fulani ke nema da mutanenmu ba. Garinmu na cikin mawuyacin hali, an takura wa mutane.”
Yan bindiga sun kuma kai farmaki a Plateau
Yan bindiga sun kai hari kan matasa masu jana'iza. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Hadimin gwamna ya tura roko ga jami'an tsaro

Jami’in ya kara da cewa an kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni, Damishi Sango, inda mace ta mutu wasu uku suka samu raunuka.

Ya ce:

“Na ji labarin harin da aka kai wa tsohon minista a gidansa dake Dakwal. Ina bakin ciki da irin wannan lamari.
“Ina jin tsohon ministan na lafiya, amma wata mace ta mutu a cikin gidan, sannan wani dan sanda da ke tsaron gidan ya jikkata.

Dantong ya bukaci hukumomin tsaro da su kara azama wajen dakile hare-haren yan bindiga domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Plateau.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai dauki kiran waya ba lokacin da aka tuntube shi kan lamarin.

Yan bindiga sun farmaki gidan tsohon minista

Kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan tsohon ministan wasanni, Damishi Sango, a ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau.

Majiyoyi sun nuna cewa maharan sun harbe wata ’yar uwarsa mace har lahira tare da jikkata ɗan sanda a gidan.

Bayan fara bincike, an gano cewa maharan sun kuma tafi da bindigar ɗan sandan da ke bakin aiki a gidan tsohon ministan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.