Sarautar Kano: Babban Malami Ya Hango Matsala, Ya Aika Muhimman Sako ga Sanusi II
- Fitaccen limamin coci, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya bayyana wahayin da aka ƙara masa kan wasu manyan mutane a Najeriya
- Ayodele, wanda ya yi kaurin suna wajen hasashen abin da zai faru a nan gaba, ya taɓo batun sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II
- Jihar Kano ta faɗa a rikicin sarauta tun lokacin da Majalisar Dokoki ta rusa masarautun biyar, Gwamna Abba Kabir kuma ya dawo da Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Yayin da ake ci gaba da rigimar sarautar Kano, fitaccen limamin cocin nan, Primate Elijah Ayodele ya ja kunnen sarki na 16, Muhammasu Sanusi II.
Primate Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya buƙaci Muhammasu Sanusi II ya yi taka tsan-tsan kuma ya bi a hankali.

Asali: Facebook
Limamin cocin ya yi wannan gargaɗi ne a wata sabuwar hira da aka yi da shi wacce jaridar Tribune Nigeria ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban malamin ya bukaci Muhammadu Sanusi II da ya yi taka-tsantsan, "musamman game abin da yake sha."
Kano: Primate Ayodele ya gargadi Sanusi II
Ayodele ya ce:
"Sarki (Sanusi Lamido), Sanusi, dole ne ya yi hankali, musamman game da abin da yake sha.”
Idan ba ku manta ba, a ranar 23 ga Mayu, 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya ba da umarnin tube Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, tare da dawo da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarki.
Gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne bayan rattaɓa hannu kan dokar da ta rusa masarautu biyar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC na yanzu, Abdullahi Ganduje ya kirkiro.
Yadda rikicin sarauta ya ɓarke a Kano
Wannan lamari dai haifar rikici tsakanin ɓangarorin biyu, Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II, kowane na bayyana kansa a matsayin sarki.
Sabuwar dokar da Gwamna Abba ya sa hannu bayan amincewar Majalisar dokoki Kano ta soke dokar masarautu ta 2019, wadda ta tsinka masarautar Kano zuwa guda biyar.
A ranar da mai girma gwamnan ya soke dokar, ya sanar da dawo da Sanusi II kan karagar sarauta.
A halin yanzu, sarkin da aka tube, Aminu Ado Bayero, yana kalubalantar tsige shi a kotu, kuma yana zaune a fadar Nassarawa a cikin birnin Kano, bayan Sanusi ya karɓi babbar fadar masarauta.

Asali: Twitter
Ayodele ya aika saƙo ga Sanusi II
Sai dai tun farko wannan rikici zuwa yanzu shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙi tsoma baki kan batun sarautar Kano duk da kiraye-kirayen da aka yi na ya shiga tsakani.
Da yake tsokacin kan halin da Sanusi II ke ciki, Primate Ayodele ya gargaɗi basaraken ya yi taka tsan-tsan musamman da abubuwan da ake kawo masa na sha.
Sanusi II ya halarci taron Tijjaniyya
A wani labarin, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya halarci babban taron Darikar Tijjaniyya a kasar Burkina Faso.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi nadin sabon Khalifan Tijjaniyya a ƙasar Burkina Faso a ranar Lahadi, 4 ga Mayu, 2025.
Sanusi II, wanda shi ne Khaliphan Tijjaniyya na Najeriya ya samu halartar wannan taron nadin bayan samun katin gayyata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng