Majalisa Ta Fara Tattauna Gyara Kundin Tsarin Mulki domin Magance Matsalolin Tsaro

Majalisa Ta Fara Tattauna Gyara Kundin Tsarin Mulki domin Magance Matsalolin Tsaro

  • Majalisar wakilan Najeriya za ta gudanar da babban taron tsaro a Abuja tare da manyan jami’an tsaron ƙasar nan don nemi mafita
  • Taron na da nufin gyara kundin tsarin mulki domin magance matsalolin rashin tsaro, ciki har da duba batun kafa ‘yan sandan jihohi
  • Ana sa ran manyan jami'an tsaro har da Mashawarcin Shugaban ƙasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su halarci taron

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki zai gudanar da wani babban taron tattaunawa a yau Litinin domin nazarin tsarin tsaron ƙasa.

Taron,wanda za a gudanar da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro (ONSA) na ɗauke da taken “Zaman lafiya da tsaron Najeriya: Dabarun da kundin tsarin mulki ke bukata.”

Majalisar dokokin Najeriya
Majalisa ta kira taro a kan rashin tsaro Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Vanguard News ta ruwaito, mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, ya ce an shirya taron ne domin tattara manyan jami’an tsaro na ƙasa don tattauna matsalolin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda za su halarci taron tsaron majalisa

Jaridar Tribune Online ta wallafa cewa manyan jami’an tsaro da ake sa ran za su halarta sun hada da Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

Sai Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, Darakta Janar na Hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed.

Mashawarcin Shugaban Najeriya, Mallam Nuhu Ribadu
Mallam Nuhu Ribadu na daga cikin wadanda za su halarci taron majalisa Hoto: Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Baya ga su, ana kuma sa ran ganin masana a fannin doka, wakilan ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin al’umma daga yankunan da ke fama da rikici da kuma ‘yan majalisar dokoki.

Majalisa na son a shawo kan rashin tsaro

Wannan tattaunawa na daga cikin manyan matakan da Majalisar ke ɗauka domin nemo mafita ga matsalolin tsaro a Najeriya ta hanyar gyara kundin tsarin mulki.

Za a duba batutuwan da suka hada da dokar kafa ‘yan sanda na jihohi da kuma sake fasalin tsarin aikin jami’an tsaro da ke faɗin kasar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai kuma Shugaban Kwamitin Gyaran Kundin Tsari, Benjamin Kalu, shi ne zai jagoranci taron.

Ana kuma sa ran samun saƙon gaisuwa daga Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen, da kuma gabatar da jawabin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ana sa ran wannan taro zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da suka mamaye sassa daban-daban na Najeriya.

Majalisa ta canja tsarin jawabin ranar dimokuraɗiyya

A wani labarin, kun ji cewa Majalisa ta amince da sabon mataki da zai wajabta wa shugaban ƙasa gabatar da jawabi ga zaman hadin gwiwar majalisa a duk ranar 12 ga Yuni.

Wannan mataki ya samo asali ne daga kudurin da Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya gabatar, don sauya yadda shugaban kasa zai gabatar da jawabin ranar dimokuraɗiyya.

A yayin zaman haɗin gwiwar da aka gudanar a ranar Alhamis, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi, wanda daga bisani ya zama wani ginshiki na kafa wannan doka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.