Matashi Ya Hau kan Dogon Ƙarfe a Kano, Ya Buƙaci Wasu Fitattun Mutane Su Je Wurin

Matashi Ya Hau kan Dogon Ƙarfe a Kano, Ya Buƙaci Wasu Fitattun Mutane Su Je Wurin

  • Wani matashi ya ɗare kan katon ƙarfen tallace-tallace a kusa da gadar Lado, titin Zariya a cikin birnin Kano yau Litinin
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya hau kan dogon ƙarfen da tsakar rana, ya yi barazanar zai faɗo idan wasu ƴan TikTok ba su je wurin ba
  • Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami'anta sun isa wurin domin jawo hankalin matashin ya sauko cikin lumana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani mutum da ba a tantance ko wanene ba ya hau wani babban allon tallace-tallace (billboard) a yankin Gadar Lado a kan titin Zariya cikin birnin Kano

Wannan al'amari dai ya ja hankalin mutane, wadanda suka kewaye wurin suna kallo tare da fargabar mutumin na iya yunƙurin faɗowa.

Wani mutumi ya ɗare allon talla a Kano.
Dakarun yan sanda sun kai ɗauki wurin da wani mutumi ya hau kan allon talla a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Jami'in hulda jama da rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin a wani gajeren saƙo da ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na rana yau Litinin, 23 ga watan Yuni, kuma ya jawo cunkoson ababen hawa da taruwar jama’a da dama a yankin.

Ƴan sanda sun gano buƙatar matashin

Abdullahi Kiyawa ya ce jami'an ƴan sanda sun isa wurin kuma yanzu haka suna ƙoƙarin ceto mutumin cikin lumana.

Sai dai kakakin ƴan sandan ya ce mutumin da ya hau allon tallar mai tsayi ya kafa sharaɗin cewa ba zai sauka ba har sai fitattun mutanen da yake bibiya a TikTok sun zo wurin.

Kiyawa ya ce:

"Yanzu haka jami'an tsaro suna kokarin ceto shi, ya ce idan 'celebrities' watau fitattun mutane da yake bibiya a TikTok ba su je wurin ba, sai ya fado. Allah ya kiyaye."

Matashi ya haddasa cunkuso a Kano

Mutumin, wanda ya kai sama da awa guda yana saman allon, yana ta wasu maganganu da ba a cika ganewa ba.

Wani ganau mai suna Habeeb Ishaq ya shaidawa jaridar Leadership cewa ya iso wurin tun kafin karfe biyu na rana, kuma ya tarar da mutumin a sama.

“Na iso nan tun misalin karfe 1:00 na rana, na same shi yana can sama. “Yana ta magana da kansa, amma saboda nisa, ba za mu iya jin abin da yake cewa ba.
"Mutane dai na ta yaɗa jita-jita iri-iri; wasu daga cikin mutanen da muka yi magana da su sun ce wai yana neman ganawa da gwamnan jiha.”
Kwamishinan yan sandan Kano.
Yan sanda sun kai ɗauki wurim da matashi ya hau kan allon talla a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Yadda mutumin ya jawo Kanawa matsala

Wani shaida mai suna Mallam Hassan ya bayyana takaici dangane da yadda lamarin ya hana jama’a da dama gudanar da ayyukansu.

"Abin takaici ne yadda abin da mutum ɗaya ya aikata ya jawo cunkoso da tsaiko ga daruruwan mutane.

"Na rasa wani muhimmin taro saboda wannan cunkoson da mutumin nan ya jawo, ya kamata gwamnati ta dauki mataki bayan ya sauko," in ji shi.

Mutum 2 sun rasu a koƙarin ciro waya daga masai

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutum biyu sun rasa rayukansu a ƙoƙarin cito wayar salula da ta suɓuce ta faɗa masai a jihar Kano.

Usman Muhammed da abokinsa Ibrahim Inuwa, dukkansu ’yan shekara 40, sun rasu yayin da suke ƙoƙarin tsamo wayar daga masai.

Hukumar kashe gobara ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa sun mutu ne sakamakon isakar guba da suka shaƙa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262