'Yan Bindiga Sun Sace Amarya Awa 2 kafin Ɗaurin Aurenta, Sun Bindige Yayanta
- Wasu 'yan bindiga sun harbe wani matashi mai shekara 27 a Osisioma a Abia, sannan suka sace kanwarsa kafin bikin aurenta
- Chibueze Joseph ya biyo kanwarsa Uzoamaka zuwa coci lokacin da ‘yan bindigar suka bude wuta, suka kashe shi
- 'Yan sanda da jami’an tsaro da mutanen gari sun fara bincike don ceto Uzoamaka da kuma gano wadanda suka aikata wannan ta’asa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umiahia, Abia - Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a Osisioma, kusa da Aba a jihar Abia inda aka kashe wani matashi.
Lamarin ya faru ne bayan harin yan bindiga wanda kuma suka sace kanwarsa kafin bikin aurenta.

Asali: Twitter
Rahoton Zagazola Makama ya gano cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare, ranar Juma’a, 20 ga Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga suka addabi jihar Abia
Jihar Abia na daga cikin jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da ke fama da hare-haren yan bindiga wanda ya jawo asarar rayuka.
Gwamnatin jihar ta sha alwashin kawo karshen yan bindiga tun farkon hawanta mulki amma har yanzu babu wani sakamako mai kyau.
Yan bindiga na yawan sace mutane da kuma kai musu hare-hare musamman a yankunan karkara da wasu birane a jihar.
Ta'addanci: Gwamna ya zargi yan siyasa
A baya, Gwamna Alex Otti ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta gano wasu ƴan siyasa da ke ɗaukar nauyin hare-haren ƴan bindiga a Abia.
Gwamna Otti ya ce bayanan da aka tattara daga nutane da wasu majiyoyi sun nuna babu hannun ƙungiyar ƴan aware IPOB a matsalar tsaron jihar.

Asali: Original
An harbe yayan amarya a Abia
Chibueze Franklin Joseph, wanda ya fito daga Owerri don halartar bikin, yana tare da kanwarsa lokacin da abin ya faru.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun tare motarsu, suka harbe Chibueze a wuyansa sannan suka jefar da shi daga mota.
Bayan haka, suka tsere da amaryar cikin wata motar bakar Toyota Sequoia, wadda ba a san lambar rajistarta ba.
Daga baya an same shi cikin jini, kuma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa bayan kokarin ceto rayuwarsa ya ci tura.
Jami'an tsaro sun bazama neman amaryar
An kai gawarsa dakin ajiye gawa na Alanwendu da ke Osisioma domin adanawa da kuma yi masa gwajin bincike.
Majiyoyi sun ce marigayin yana cikin murna sosai kan bikin aurar da kanwarsa, kuma shi ke jagorantar shirye-shirye.
Bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda, jami’an tsaro na gari da al’umma suka shiga aiki don gano inda take.
An hallaka baban ango a harin Plateau
Mun ba ku labarin cewa ana cikin jimami kan kisan gillar da wasu gungun mutane suka yi wa masu zuwa ɗaurin aure daga Kaduna zuwa Plateau.
A yayin farmakin da ka kai wa mutanen, an hallaka mutum 12 har lahira yayin da aka jikkata wasu da dama.
Bayanai sun nuna cewa daga cikin mutanen da aka kashe har da mahaifin ango da wasu daga cikin ƴan uwansa.
Asali: Legit.ng