Innalillahi: Walkiya ta kashe mutane 27 yayin da da yawa kuma suka jikkata

Innalillahi: Walkiya ta kashe mutane 27 yayin da da yawa kuma suka jikkata

- Walkiya ta yi ajalin a kalla mutane 27 kuma ta raunata mutane da yawan gaske a kasar Pakistan

- Hakan ya faru ne sakamakon mamakon ruwan saman da aka fara tun daga ranar Alhamis har Juma’a

- Masana a harkar yanayi sun ce hakan ya faru ne sakamakon dumamar yanayi, abinda ya kamata a dau matakin gaggawa a kai

Jami’ai sun ce walkiya kashi daban-daban ta kashe a kalla mutane 27 kuma ta raunata mutane da yawa a yankuna daban-daban na kudancincin kasar Pakistan. Hakan ya faru ne a sa’o’I 24 da suka gabata, kamar yadda wata kafar yada labaran kasar ta ruwaito a safiyar Juma’ar nan da ta gabata.

Saeed Ghani, mai Magana da yawun gwamnatin yankin yace, tuni hukumomi suka yi fitowar gaggawa don tseratar da mutane zuwa hamadar Thar da ke yankin Sindh bayan aukuwar abun cikin dare.

Ya kara da cewa, mutane da yawa da suka hada da mata da kananan yara na karbar kulawa daga asibitoci.

Sun samu raunika ne daga walkiyar da kuma gini da suka dinga faduwa sakamakon ruwan sama.

KU KARANTA: Innalillahi: Bidiyon yadda wani sojan Najeriya ya tono jariri sabuwar haihuwa da aka binne da ranshi

Aslam Kazimi, daya daga cikin jami’ai masu tseratar da mutanen yace, gunduma uku lamarin ya shafa inda da suka hada da Tharparkar, Mirpurkhas da Sukkur, inda aka yi ruwan saman daga ranar Alhamis har zuwa Juma’a.

Ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, fari da sauransu ne suka yi kaka gida a kasar Pakistan din, abinda ke hana ingantacciyar iska zagayawa a cikin shekarun nan.

Kwararre akan yanayi, Chaudhry Qamar Zaman yace, hakan ya faru ne hadi da kasashen da ke makwabtaka dasu masu tarin masana’antu irinsu: China da India. Dole ne kuwa Pakistan ta fuskanci matsalar dumamar yanayi.

Zaman ya kara da cewa, dole ne kasar da mutanenta su karbi sakamakon kuma su yi kokarin daukar matakin gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel