Borno: Budurwa Ƴar Ƙunar Baƙin Wake Ta Hallaka Mutane 24 a wurin Cin Abinci
- Akalla mutane 24 sun mutu da wata budurwa 'yar kunar bakin wake ta tarwatse a wajen cin abinci a Konduga, Jihar Borno
- An kai harin da misalin karfe 10:00 na dare, inda gawar ‘yar kunar bakin waken ta tarwatse gaba daya, sai kai kadai aka tsinta
- Jami’an tsaro sun killace yankin, an dauki gawarwakin zuwa dakin ajiye gawa, yayin da raunana ke samun kulawa a asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Konduga, Borno - Wata budurwa yar kunar bakin wake ta yi ajalin mutane da dama a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Akalla mutane 24 aka ruwaito sun mutu bayan wata mace yar kunar bakin wake ta kai hari wanda ya daga hankulan al'umma da ke yankin.

Asali: Original
An hallaka mutane a harin bam a Borno
Rahoton TheCable ya ce lamarin ya faru ne a wajen cin abinci a karamar hukumar Konduga da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun tabbatar da cewa harin ya faru ne a yankin Tafkin Chadi da misalin karfe 10:00 na daren ranar.
Majiyar ‘yan sanda ta ce ‘yar kunar bakin waken ta tarwatsa nakiya a wajen cin abinci, inda harin ya jikkata mutane da dama.
An ce gawar ‘yar kunar bakin waken ta tarwatse gaba daya, sai kai kadai ne aka samu daga cikin sassan jikinta wanda ya rage.
Daga bisani an kai gawarwakin zuwa dakin ajiye gawa, yayin da raunana ke karbar kulawa a asibiti mafi kusa da wajen harin.

Asali: Original
Harin bam: Matakin da jami'an tsaro suka ɗauka
Wata hadakar jami’an tsaro ta sojoji da ’yan sanda, CJTF da mafarauta sun kai ziyara wajen harin domin bincike da daukar mataki.
An killace yankin gaba daya, an kuma kara tsaro a garin Konduga don hana sake kai irin wannan mummunan harin.
Rundunar ’yan sandan Borno bata amsa kiran waya daga yan jaridu ba kan lamarin, kamar yadda rahoton Punch ya tabbatar.
Yadda Konduga ke fama da hare-haren bam
Amma an ce yan sanda na cikin binciken da aka fara kai tsaye domin gano bakin zaren da dakile faruwar haka a gaba.
Wannan ba shi ne karon farko ba da masu kai harin bam ke hallaka mutane a karamar hukumar Konduga da ke jihar a Arewacin Najeriya.
Ko a watan Agusta 2024, mutane akalla 17 sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai kasuwa a garin Konduga.
Sojoji sun lalata masana'antar hada bam a Borno
Mun ba ku labarin cewa rundunar sojin sama ta Najeriya watau NAF ta kai farmakin sama kan wani wuri da ake amfani da shi wajen hada bama-bamai.
Rahotanni suka ce an kai harin a yankin Tumbuktu da ke jihar Borno bayan samun bayanan sirri cewa 'yan ta'adda suna kera makamai a wurin.
Nasarar da sojojin suka samu a kan 'yan ta'addan ya biyo wasu nasarorin da aka samu a kwanakin wajen dakile 'yan ta'adda da suka addabi yankuna a Borno.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng