Harin bom ya kashe mata da miji a Borno

Harin bom ya kashe mata da miji a Borno

Wani miji da matarsa ​​sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai kauyen Kafan Ruwa na karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa harin wanda ya rusa gidaje ya kuma ya raunata mutane dama da ba kawo yanzu ba a san adadinsu ba.

Kauyen Kafan Ruwa galibin al'ummar masunta ne wanda 'yan kabilar Hausawa suka fi rinjaye a cikinsa.

Yana da 'yar gajeriyar tazara da hedikwatar karamar hukumar Konduga wanda ya ke da tazara ta akalla nisan tafiya ta kilomita 40 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, harin ya auku ne da misalin karfe 12.30 na daren ranar Lahadi, yayin da wata mace 'yar kunar bakin wake daure da bam a jikinta ta kutsa cikin gidajen al'umma.

Harin bom ya kashe mata da miji a Borno
Harin bom ya kashe mata da miji a Borno
Asali: UGC

Yayin da aka tuntubi mataimakin jami'in hulda da al'umma na hukumar 'yan sandan jihar, Yakubu Muhammad, ya bayar da tabbacin aukuwar harin.

Sai dai ya ce ba zai iya bayar da wani karin bayani ba dangane da adadin rayukan da suka salwanta da sauran asarar da harin ya yi sanadi.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, mayakan Boko Haram sun kashe akalla rayuka 16 a wani hari da suka kai sansanin 'yan gudun hijira da ke arewacin kasar Kamaru a cewar wani jami'i da ya ba da sanarwa.

"A halin yanzu yawan wadanda suka rasu sun kai 16, har yanzu ba a tabbatar da cewa ko Boko Haram bace da alhakin harin ba," inji Mahamat Chetima.

Wani dan siyasa da ke yankin ya kwatanta jama'ar wurin da irin mutanen da ke boyewa idan maharan Boko Haram sun bayyana.

KARANTA KUMA: Fashewar Bam ya kashe yara shida a Burkina Faso

Tarihi ya tabbatar da cewa ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ya samo asali ne tun a shekarar 2009 ina har kawo yau take ci gaba da addabar yankin arewa maso gabas na Najeriya.

Suna kai hari wurare da dama don satar dabbobi da kayayyakin abinci.

"A makonni kadan da suka gabata, an samu zaman lafiya amma daga baya sun yi amfani da ilimin sanin hanyar idan suka tsallake jami'an tsaro. Sun bamu mamaki," shugaban ya kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel