Wani Mutum Ya Tono Gawar 'Yar Uwarsa a Kabari domin a Ba Shi Kudi a Banki

Wani Mutum Ya Tono Gawar 'Yar Uwarsa a Kabari domin a Ba Shi Kudi a Banki

  • Wani mutum a kasar India ya ba da mamaki da ya tono gawar 'yan uwarsa a kabari bayan ta zama kwaragwal domin karbar kudin da ta bari
  • Rahotanni sun nuna cewa bankin ya ki ba shi kudin da ta bari ne har sai ya nuna shaidar cewa ta mutu, saboda haka ya tono gawarta
  • 'Yan sa'o'i bayan bayyanar mutumin da gawar, bankin ya yi karin bayani game da abin da aka bukace shi ya yi maimakon tono gawar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

India - Wani dattijo a gabashin kasar Indiya ya girgiza ma’aikatan banki da abokan hulda bayan ya tono gawar ‘yar uwarsa domin tabbatar da mutuwarta da kuma samun damar karbar kudin da ke asusunta.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a yankin Malipasi da ke gundumar Keonjhar a jihar Odisha, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan bindigogi da wukaken da aka so kashe Trump da su

Gawar da aka tono a India
Wanda ya tono gawar 'yar uwar shi da dan sandan kasar India. Hoto: @OBSERVERX_HQ|Getty Images
Source: Twitter

A wani sako da ya wallafa a X, bankin Indian Overseas ya bayyana cewa ba a nemi mutumin ya kawo gawar 'yan uwar shi da ta mutu ba.

Wanda ya gono gawar 'yar uwarsa

Mutumin mai suna Jitu Munda daga kauyen Dianali ya je reshen bankin Odisha Grameen da ke yankin Patana domin cire kusan rupiya 20,000 daga asusun ‘yar uwarsa Kalara Munda, wadda ta rasu.

Sai dai ma’aikatan bankin sun bukaci takardun da ake bukata da za su nuna tabbas cewa ta mutu kafin su aiwatar da bukatar.

A wani mataki mai ban mamaki, Munda ya tono kwarangwal din ‘yar uwarsa ya kai shi bankin a matsayin hujjar mutuwarta, abin da ya razana duk wanda ke wurin.

“Na gaya musu ta rasu, amma ba su saurare ni ba. Suna cewa sai na kawo mai asusun kafin a ba ni kudin. Saboda takaici ne na tono kabarin na kawo kwarangwal dinta domin tabbatar musu cewa ta rasu,”

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Daga kwanciya barci, an tarar da gawar fitaccen jarumin fim a Najeriya

In ji shi.

Bayanin 'yan sandan India

Lamarin ya sa jami’an ‘yan sanda daga yankin Patana suka kai ziyara bankin bayan samun rahoto, wani jami’in ‘yan sanda, Kiran Prasad Sahu, ya ce hakan ya nuna ba a fahimci juna ba.

“Bai fahimci ma’anar magaji ko wanda zai karbi kudi a asusu ba bayan mutuwar mai shi. Ma’aikatan bankin sun kasa bayyana masa yadda ake karbar kudi daga asusun mamaci,”

In ji Sahu.

Bayan shigar ‘yan sanda, ma’aikatan bankin sun tabbatar wa Munda cewa za a taimaka masa wajen bin hanyoyin doka domin samun kudin.

Wani banki a kasar India
Mutane na wucewa ta kusa da banki a India. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daga bisani, an mayar da gawar aka sake birne ta a kabari a gaban jami’an ‘yan sanda kuma an bi hanyoyin da suka dace wajen ba shi kudin.

Ga bidiyon mutumin da shafin World Observer ya wallafa a X:

India ta ki karbar jakadan Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu kasashen duniya sun ki karbar jakadun da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura masu.

Kara karanta wannan

Yana ajiye mukamin minista, Tuggar ya fadi abin da ya jawo ta'addanci a Bauchi

An ce India na cikin kasashe da suka nuna shakku kan karbar jakadan Najeriya saboda an tura shi kasa da shekara biyu wa'adin Tinubu ya kare.

Kasashe da dama sun kafa sababbin dokoki game da karbar jakadu daga kasashen da shugabannin su suka kusa sauka daga mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng