Zanga Zanga Ta Barke kan Ƙoƙarin Ƙaƙabawa Al'umma Sarki da Karfi da Yaji
- Al’ummar Ukhomuyio a Okpella a Edo sun yi zanga-zanga kan nadin Michael Sado da suka ce ya saba da dokokin gargajiya na sarauta
- Cif Charles Adogah ya ce kabilar Oteku kadai ke da hurumin zabar Sarki bisa kulawar dagacin gari kamar yadda doka ta tanada
- Gwamnatin jihar Edo ta ce an yi latti kan lamarin, amma al’umma sun bukaci a dakatar da nadin tare da sakin wadanda aka kama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Mambobin al’ummar Ukhomuyio a jihar Edo sun cika tituna domin gudanar da zanga-zanga.
Mutane da ke Okpella a karamar hukumar Etsako ta Gabas a Edo, sun gudanar da zanga-zanga a kokarin ƙaƙaba musu sabon Sarki.

Asali: Original
Nadin sarauta: Zanga-zanga ta barke a jihar Edo
Rahoton Punch ya ce al'umma sun fito zanga-zanga ne kan nadin Michael Sado a matsayin Okuokpellagbe na Okpella.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa tsarin zaben ya sabawa tanadin dokar gargajiya da ke tsara yadda ake gadon kujerar sarautar gargajiya a yankin.
A cewarsu, wani bangare da ba a amince da shi bisa doka ba ne ya zabi Sado, kuma hakan ya sabawa yadda ake gudanar da nadin sarki.
Edo: Abin da masu zanga-zanga suka ce
Da yake magana da yawun masu zanga-zangar, Obodeanokpella, Cif Charles Adogah, ya ce doka ta fayyace wanda ya dace da ya zabi sabon sarki.
Cif Adogah ya nuna damuwa kan wani tsarin daban da ake cewa Gwamna Monday Okpebholo ya amince da shi wanda bai dace da al’ada ba.
Al’ummar sun bukaci a mutunta tsarin gargajiya tare da kira ga gwamnati da ta girmama tanadin doka domin tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce:
“Manyan dattawan yankin da suka fito sun yi magana a kan batun an kama su, an tsare su kuma ana ci gaba da tsoratar da su.
Ya roki Gwamna Okpebholo da ya dakatar da nadin Sado da kuma soke tsarin da ya haifar da rikici da rashin jituwa a cikin al’umma.
“A bar kauyen Komunio na gidan sarauta Oteku su gudanar da zaben Sarki ba tare da tsoma baki daga waje ba.
"Ana gudanar da tsarin zaben bisa tanadin dokar gargajiya, kuma dole ne a kiyaye wannan hanya da doka ta shimfida."

Asali: Twitter
Martanin gwamnatin jihar Edo kan lamarin
Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da sarautar gargajiya a Edo, Lucky Eseigbe, ya ce masu yin zanga-zangar yanzu sun makara.
Eseigbe ya bayyana cewa Gwamna ya amince da nadin Sado, wanda ya fito daga cikin al’ummar da suka gabatar da sunansa.
An tasa keyar Sarki zuwa gidan kaso
Kun ji cewa wata kotu a Ede a jihar Osun, ta bayar da umarnin tsare wani basarake da aka dakatar, Jimoh Abdulkabir, bisa zargin batanci.
Ana zargin Abdulkabir da yada kalaman batanci da barazana a manhajar WhatsApp kan wani Alhaji Adam Akindere.
Lauyansa ya nemi beli, yana cewa yana fama da ciwon gyambon ciki, amma kotu ta dage sauraron kara zuwa 19 ga Yuni, 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng