'Ku Sake Fentin Kodaddun Gidajenku': Gwamna Ya ba Mazauna Birane Wa'adi

'Ku Sake Fentin Kodaddun Gidajenku': Gwamna Ya ba Mazauna Birane Wa'adi

  • Gwamnatin Anambra ta umurci mazauna gidaje da suka lalace su yi fentin gidajensu su kafin 1 ga Yuli 2025, ko a ɗauki mataki a kansu
  • Kwamishinan muhalli, Dr. Felix Odimegwu, ya ce dokar tana nufin kyautata kyan gani da kiyaye dokokin muhalli na jihar Anambra
  • Gwamnatin za ta fara sintiri daga 1 ga Yuli domin tabbatar da biyayya, inda aka bukaci kowa ya gyara gidansa da ke cikin biranen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta bayar da umarni kan sake fasalin gidaje a biranen jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Gwamnatin ta umarci mazauna da masu gine-ginen da suka lalace ko suka dusashe da su fente gidajensu kafin 1 ga Yulin 2025.

An taso gwamna a gaba kan sabon umarni a Anambra
Gwamna Soludo ya umarci sabon fente a gidajen Anambra. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Asali: Facebook

Umarnin sake fenti a gidajen biranen Anambra

Wannan umarni ya fito ne ranar Alhamis a wata sanarwa da kwamishinan muhalli, Dr. Felix Odimegwu, ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an ba da umarnin ne domin inganta tsaftar birane da aiwatar da dokar muhalli domin kawata biranen musamman kan hanyoyin da jama'a ke gani.

Ta ce aikin fente gini zai fi mayar da hankali ne a wuraren da mutane suka fi yawa kamar Onitsha, Awka, Nkpor, Nnewi da Ekwuluobia.

Kwamishinan ya ce dole ne mutanen da ke wadannan yankuna su feshe gidajensu, musamman waɗanda suka lalace cikin shekaru goma da suka wuce.

Sanarwar ta ce:

“Anan muna sanar da mazauna da masu gida a wuraren da ke kan hanyoyin wucewar jama’a cewa duba na musamman zai fara nan take.
“Wannan aiki yana nufin ƙarfafa gine-gine, inganta kyawun gari da ƙara sararin kore a jihar kamar yadda dokar muhalli ta tanada."

Felix ya kuma bayyana cewa daga 1 ga Yuli, hukumomin da ke da alhakin kula da doka za su fara aiki don tabbatar da mutane sun bi umarni.

“Don haka ana bukatar kowa ya gyara, ya fesa gidansa idan ya lalace, musamman waɗanda ke inda jama’a ke yawan gani."

- Cewar sanarwar

Sabuwar doka a jihar Anambra ta bar baya da kura
An bukaci mazauna biranen Anambra su sake fentin tsofaffin gidajensu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Musabbabin umarnin sake fenti a gidajen Anambra

Dr. Odimegwu ya ce burin gwamnati shi ne kyautata birane da tsafta, ya kuma roƙi al’umma da su haɗa kai domin cimma wannan buri.

Ya ce:

“Za mu iya samun Anambra mai tsafta, kyau da kore idan muka haɗa hannu wajen inganta kyan biranenmu."

Gwamnatin Charles Soludo za ta fara sintiri daga 1 ga Yuli domin tabbatar da biyayya ga dokar inda aka bukaci kowa ya gyara gidansa.

Gwamna ya ƙaƙabawa APC da jam'iyyu haraji

Mun ba ku labarin cewa jam'iyyun siyasa 16 a Anambra za su biya N800m don samun izinin gudanar da yakin neman zabe da kafe allunan tallata 'yan takara.

Kowace jam'iyya za ta biya N50m kafin fara yakin neman zabe, umarnin da ya haifar da cece-kuce daga jam'iyyu, irinsu LP da APC APC.

Ana zargin gwamnatin Anambra da yunkurin rufe muryoyin 'yan adawa yayin da suka ce hakan kuma ba zai hana APGA faduwa zabe ba da za a yi a karshen shekarar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.