Waka Ta 2 Ta Fito, Rarara Ya Yi Kaca Kaca da Shugaban Nijar, Tchiani a Bidiyo
- Mawaki Dauda Kahutu Rarara, ya fitar da waka ta biyu a jerin wakoki tara na caccakar shugaban Nijar, Abdurrahmane Tchiani
- Sabuwar wakar Rarara mai taken "Mun yi tir da kai Chali" ta soki mulkin Janar Tchiani, ya ce al'ummar Nijar ba su amince da shi ba
- A hannu daya kuma, Kosan Waka ya fitar da waka mai taken "Maza Maganin Maza Tchiani," ya gwarzanta shugaban na Nijar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitaccen mawakin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya sake sakin wata wakar caccakar shugaban Nijar, Mai girma Janar Abdurrahmane Tchiani.
Wannan waka ta biyu da ya fitar, cika alkawarin da ya dauka ne na sakin wakokin caccakar Tchiani har guda tara, domin adawa da mulkin da yake yi a Nijar.

Asali: Facebook
Rarara zai saki sabuwar wakar Tchiani
Rarara ya shirya sakin sabuwar wakar Tchiani ta biyu a ranar Talata, 11 ga Fabrairu a Youtube kamar yadda Rabi'u Garba Gaya ya sanar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabi'u Gaya, mai magana da yawun mawakin ya ce Rarara zai saki sabuwar wakar ne da misalin karfe 9:00 na dare.
A cikin taba-ka-lashe na wakar da Rarara ya dauka a bidiyo, an ji mawakin yana caccakar shugaban Nijar, Janar Tchiani.
Rarara ya kira Tchiani da 'matsoraci'
Sai dai, mawakin bai kama sunan Tchiani kai tsaye ba, inda ya ke kiransa da 'Chali' kamar yadda ya yi a wakarsa ta farko mai taken: Chali Motar Kaya.
A cikin sabuwar wakar, mai taken 'Mun yi tir da kai Chali,' anji mawaki Rarara yana cewa al'ummar Nijar sun yi tur da shugaban kasar nasu.
Rarara ya yi ikirarin cewa shugaba Tchiani shi ne babban makiyin kasar Nijar yayin da ya jefe da shi da kalmar "rago" kuma "matsoraci."
Kalli bidiyon a nan kasa:
Kosan Waka ya fara kare shugaban Nijar
A hannu daya kuma, mawakin siyasar nan, Kosan Waka, ya fara yin wakokin martani ga Dauda Rarara tare da kare shugaban Nijar, Janar Tchiani.
A wata waka da ya fitar mai taken "Maza Maganin Maza Tchiani," an ji Kosan Waka yana gwarzanta Tchiani da zama shugaba mafi soyuwa a Nijar.
A bidiyon da wani Aminu Nagidan Soja Gwale ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kosan Waka ya tattara duk masu zage-zage, da yiwa Tchiani batanci ya zage su tatas.
Kalli bidiyon a nan kasa:
'Rarara ba shi da ra'ayin kashin kansa' - Tukur
A zantawar Legit Hausa wani dalibin adabi, Tukur Muh'd Abdullahi, ya yi ikirarin cewa wakokin da Rarara ya ke yi wa shugaban Nijar sun sabawa gwadaben adabi.
Tukur Muh'd Abdullahi ya ce:
"Rarara fa idan sojoji zasu karɓi ikon Nigeria nan da wata ɗaya, zai yi musu waƙa na nuna mulkin soja yafi demokradiyya, da nuna goyon baya a gare su dari bisa dari.
"Adabin Rarara na tafiya da masu mulki ne masu faɗa aji, bashi da wata alƙibla a ra'ayin ƙashin kai.
"Dan haka Rarara baya cikin mawaƙa masu burgeani, dan bashi da ra'ayin ƙashin kansa, yana da ra'ayin tafiya da masu faɗa aji.
"Haka Rarara ba ya cikin mawaƙa masu bani haushi, dan baya barin kansa ya kulle akan buƙatar kansa, wannan kuma kusan halin mu ƴan Nigeria ne."
Malam Tukur ya ce mafi akasarin mawakin siyasar yanzu, "idan ka cire Aminu Ladan Abubakar," suna wakoki ne ba bisa ka'idar adabin ba.
Rarara ya ba Tchiani wa'adin kwanaki 20
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya ba shugaban Nijar, Janar Abdurrahmane Tchiani wa'adin kwanaki 20 ya mika mulki ga farar hula.
Rarara ya ce zai fara fitar da wakokin caccakar Tchiani madamar bai mayar da mulkin Nijar ga Mohammed Bazoum ko a fara shirin sabon zabe ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng