Bidiyon Yadda Rarara Ya Cashe da Sabuwar Waƙa a Liyafar da aka Shiryawa Tinubu a Katsina
- Fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya saki sabuwar waƙar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Rarara ya ƙayatar da Shugaba Tinubu, Gwamna Dikko Umar Raɗɗa da manyan ƴan siyasa a wurin liyafar da aka shirya a Katsina
- Gwamnatin Katsina ta shirya liyafar ne domin girmama Tinubu wanda ya kai ziyarar kwanaki biyu a jihar, abin da ba a taba gani ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - A jiya Juma'a, 2 ga watan Mayu, 2025, Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara ziyarar kwanaki biyu a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
Shugaba Tinubu ya dura a Katsina ne da yammaci kuma ya samu tarba daga Gwamna Dikko Raɗɗa da wasu gwamnonin Arewa da ƙusoshin APC.

Asali: Facebook
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta wallafa a X, ta ce Tinubu zai ƙaddamar da muhimman ayyuka tare da halartar taruka yayin zamansa a Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta shirya wata liyafa ta musamnan a daren Juma'a domin maraba da mai girma Tinubu da girmama shi.
Rarara ya saki sabuwar wakar Tinubu
A wurin wannan liyafa, fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara ya saki sabuwar waƙar Tinubu mai taken ‘Omo Ologo’ (yaro mai nasara da ɗaukaka).
A wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, an ga Rarara ya fito kan dandamali yana rera waƙar yayin da shugaban kasa ke zaune yana sauraro.
Wani mai amfani da shafin X, Imran Muhammad ya wallafa bidiyon yadda Dauda Kahutu Rarara tare da wasu mata biyu suka cashe a wurin liyafar.
Waƙar Rarara ta kayatar da Bola Tinubu
Bidiyon ya nuna cewa waƙar ta ƙayatar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ganin yadda ya riƙa tafi yana murmushi a wurin da yake zaune tare da Gwamna Dikko Raɗɗa.
Rarara ya yi amfani da kalamai a harshen Hausa, Turanci da kuma Yarbanci wajen wasa Tinubu, lamarin da ya ƙayatar da duka mahalarta liyafar.
Ana sa ran shugaban ƙasa zai ci gaba da ƙaddamar da ayyuka kamar yadda aka tsara yau Asabar, 3 ga watan Mayu, 2023.

Asali: Facebook
Haka nan kuma ana sa ran Shugaba Tinubu zai halarci ɗaurin auren ɗiyar Gwamna Malam Dikko Raɗɗa, wanda za a yi yau Asabar.
Wannan ziyara dai ita ce ta farko Tinubu ya kawo Katsina, mahaifar tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, ita ce ta farko tun bayan hawa mulki a mayun 2023.
Tinubu ya dura kan masu shirin tarwatsa ƙasa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara ziyarar kwanaki biyu a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
A wurin faretin maraba da sojoji suka shirya, Shugaba Tinubu ya yi gargaɗi da babbar murya ga masu yunƙurin ruguza Najeriya ta hanyar tayar da zaune tsaye.
Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta sunkaya gaban masu kulla mata makirci ba, za ta samar da kayan aiki ga sojoji don magance dukkan kalubalen tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng