Innalillahi: Tsohon Atoni-janar a Jihar Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya da Shekaru 81

Innalillahi: Tsohon Atoni-janar a Jihar Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya da Shekaru 81

  • Gwamna AbduRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya kadu da rasuwar tsohon Atoni-janar a jihar
  • A jiya Lahadi 7 ga watan Janairu Allah ya karbi rayuwar Alhaji Alarape Salman ya na da shekaru 81 a duniya
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakayeya fitar a jiya Lahadi 7 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Tsohon Atoni-janar na farko a jihar Kwara, Alhaji Alarape Salman ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a jiya Lahadi 7 ga watan Janairu a birnin Ilorin da ke jihar ya na da shekaru 81 a duniya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Don burge Bankin Duniya: An tona asirin dalilin Tinubu na kara farashin mai da wutar lantarki

Tsohon Atoni-janar na jihar Arewa ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 81 a duniya. Hoto: Alhaji Alarape Salman.
Asali: Twitter

Mene gwamnan Kwara ke cewa kan rasuwar?

Gwamna AbduRahman AbdulRazaq ya nuna alhininsa kan rasuwar inda ya ce tabbas an tafka babban rashi, cewar News Now.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakayeya fitar a jiya Lahadi 7 ga watan Janairu a Ilorin.

Gwamnan ya bayyana irin gudunmawar da marigayin ya bayar a lokacin da ya ke rike da mukamin kwamishinan Shari'a.

Ya ce irin gudunmawar da Salman ya bayar ba za ta misaltu ba a jihar da ma kasar baki daya, The Metro Lawyer ta tattaro.

Wace gudunmawa marigayin ya bayar a jihar?

AbdulRazaq ya tura sakon jaje ga Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari da kuma Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) kan wannan babban rashi.

Sanarwar ta ce:

"Ina jajantawa Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari da masarautar Ilorin da kuma Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) kan wannan rashi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali bayan tirela ta murkushe sabon dan sanda a bakin aiki a jihar Arewa, bayanai sun fito

"Tabbas marigayin ya ba da gudunmawa sosai ga Ilorin da kuma jihar da ma bangaren shari'a a kasar."

Ambassada Anka ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, Fitaccen dan siyasa a Najeriya, Ambasada M. Z Anka ya riga mu gidan gaskiya a jihar Sokoto.

Marigayin wanda asali dan jihar Zamfara ne ya rasu bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Anka shi ne mahaifi ga kwamishinan harkokin lafiya a jihar Zamfara, Dakta Aisha M. Z Anka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel