Kwanaki da Sukar Abba, Masarauta Ta Sutale Rawanin Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano

Kwanaki da Sukar Abba, Masarauta Ta Sutale Rawanin Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano

  • Masarautar Gaya ta sanar da cewa ta janye nadin Wazirin da ta yi wa tsohon Sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji
  • Jami'in yada labaran karamar hukumar Gaya, Munzali Muhammad Hausawa ya tabbatar wa Legit cewa an tsige shi ne bisa wasu dalilai
  • Duk da ba a bayyana dalilan ba, an dauki matakin kwanaki kadan bayan Usman Alhaji ya zargi gwamnatin Kano da rashin alkibla

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Masarautar Gaya a Kano ta tsige tsohon Sakataren Gwamnati jihar, Alhaji Usman Alhaji daga sarautar Wazirin Gaya.

Alhaji Usman Alhaji ya rike mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG) a lokacintsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma jigo ne a jam’iyyar APC.

Masarautar Kano ta tsige Wazirinta
Masarautar Kano ta tsige Alhaji Usman Alhaji daga sarauta Hoto: Kamal Dalhatu Gaya/Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ko da yake masarautar ba ta bayyana cikakken dalilin janyewar ba, matakin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan tsohon SSG ya soki gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Usman Alhaji ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta NNPP da rashin tsari, kwarewa, da kuma gaza fito da ingantattun manufofin mulki.

Usman Alhaji ya ce gwamnati mai-ci ta karbo bashin $6m, zargin da ta karyata tun tuni.

Kano: Masarautar Gaya ta kori Wazirinta

A wata tattaunawa da Legit, Jami’in Yada Labarai Gaya, Munzali Muhammad Hausawa, ya tabbatar da tsige Wazirin, kamar yadda Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya shaida masa.

Ya bayyana cewa matakin ya fara aiki nan take, kuma an yanke shawarar ne bisa “wasu dalilai da ba a fayyace wa jama'a ba.

Da aka tambaye shi ko wannan mataki yana da nasaba da kalaman da tsohon SSG ya yi na sukar gwamnati, Munzali ya ce:

“Hakan ba zai iya sa wa ba, domin kuwa kin san ita harkar masarauta biyayya take ga gwamnati. Shi mai sarauta uba ne na kowa. Wannan ne zai iya nuna miki cewa ita masarauta babu ruwanta da abin nan.”

Ya kara da cewa:

“Su masarauta ba sa so kana cikin masarauta, ka rika fita daga hurumin da ka ke na uban al’umma ka shiga wata harka.'"
"Batun sukar gwamnati da tsohon SSG ya yi harka ce ta siyasa kurum, amma ita masarauta babu ruwanta da haka.”

Masarautar Gaya ta godewa tsohon SSG na Kano

Masarautar ta Gaya ta nuna godiya ga Alhaji Usman Alhaji bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban al’ada da martabar masarautar yayin da yake rike da mukamin Wazirin Gaya.

Wasikar ta bayyana cewa:

“Wannan mataki yana nuna yadda masarauta ke kokarin kare mutunci da kima da darajar sarautun gargajiya bisa al’adu da dokokin da aka saba bi.”

Martanin Gwamnatin Kano ga tsohon SSG

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta karyata zargin Alhaji Usman Alhaji da ke cewa ta sake karɓar sabon bashi da ya kai $6.6m.

Zargin ya fito ne daga wata ƙungiya mai suna APC Patriotic Volunteers, ƙarƙashin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji.

Dr. Hamisu Sadi Ali, Darakta Janar na Hukumar Kula da Basussuka ta Jihar Kano, ya ce babu wani bashi da aka karɓo daga watan Yuni zuwa Disamba 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.