‘Ina Suka Shiga’: An Taso Gwamna Abba Kabir a Gaba kan Karbar Bashin $6.6m
- Kungiyar 'APC Patriotic Volunteers' ta zargi gwamnatin Kano da karɓar bashin $6.6m ba tare da wani aikin da aka yi da shi ba
- Shugaban kungiyar, Usman Alhaji, ya ce rahoton DMO ya tabbatar cewa an karɓi bashin daga watan Yuni zuwa Disamba, 2023
- Ya kuma zargi gwamnati da yin almubazzaranci da N5.1bn na kudin muhalli, duk da rashin wani aiki da aka gani an yi da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An taso gwamnatin Abba Kabir Yusuf a gaba kan karɓar makudan miliyoyin daloli bashi a jihar Kano.
Kungiyar 'APC Patriotic Volunteers' ta zargi gwamnatin jihar da karɓar bashin $6.6m daga ƙasashen waje.

Asali: Facebook
Zarge-zargen cin bashi kan gwamnatin Abba Kabir
Shugaban ƙungiyar, Usman Alhaji ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Laraba, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ruwaito cewa taron manema labaran na kungiyar ya mayar da hankali kan aikin gwamnatin NNPP a cikin shekaru biyu.
A cewar Alhaji, kungiyar na da cikakken bayani cewa rahoton Hukumar DMO ya tabbatar da gwamnatin Abba Kabir ta karɓi bashin.
Kungiyar ta ce duk da wannan bashin, gwamnatin jihar ta ciwo ƙarin lamuni daga wasu wurare, amma babu wani aiki da aka gani.
Ya ce:
“Mun samu tabbaci daga DMO cewa daga watan Yuni zuwa Disamba 2023, an karɓi bashin $6.6m daga waje kawai.
“Muna bukatar gwamnatin jihar ta bayyana yadda aka kashe wadannan manyan kudi."

Asali: Facebook
An kalubalanci Gwamna Abba Kabir Yusuf
Mista Alhaji ya kalubalanci gwamnatin jihar da ta tabbatar da gaskiyarta ta hanyar bayyana cikakken adadin bashin da ake bin ta.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin Abba Kabir da ɓarnatar da kudaden muhalli da gwamnatin tarayya ta aiko da yawansu ya kai N5.1bn.
Alhaji ya ce binciken da suka yi ya tabbatar da cewa Kano ce ta fi karɓar kudin da ya shafi muhalli domin warware matsaloli kan haka, Daily Post ta ruwaito.
“Daga Yuni 2023 zuwa Yuni 2024, Kano ta karɓi N2.1bn domin magance haɗurran muhalli da sauran matsalolinta.
“Wani ƙarin N3bn na musamman ma Shugaba Tinubu ya amince da shi domin kowace jiha ta magance bala’o’i da ambaliya.
“Abin takaici babu wani shaidar yadda aka yi amfani da kudin wajen yaki da ambaliya."
Ana zargin gwamnatin Abba Kabir da almundahana
Kungiyar ta ce bisa bincikenta, gwamnatin Abba Kabir ba ta yi aiki yadda ya kamata ba a cikin shekaru biyu da ta shafe a mulki.
“Bayan mun duba aikin gwamnatin Kano a cikin mulkin NNPP, mun fahimci akwai ƙarya da rashin gaskiya da yaudara sosai.
An zargi hadimin gwamna da cin amana
Mun ba ku labarin cewa dan majalisar tarayya, Tijjani AbdulKadir Jobe ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf kan cigaba da mu'amala da Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Hon Jobe, wanda dan majalisar yankin kakakin gwamnan ne, yana zargin hadimin da hada kai da 'ya'yan tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje.
Ya ce Sanusi na karbo kuɗi daga bangaren Ganduje tare da kuma korar 'yan NNPP a mazabunsu, wanda ya ce zai iya cutar da jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng