An Kashe Sojojin Najeriya a Harin da Aka Kai Benue, Mutum 6,527 Sun Rasa Muhalli
- Hare-haren 'yan bindiga a Benue sun yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 100 da raba mutane 6,527 da muhallansu, a cewar NEMA
- Rahoto ya nuna cewa an kashe sojoji biyu da jami'in NSCDC daya a harin kwanton bauna a jihar, inda aka kwantar da mutum 46 a asibiti
- NEMA ta kafa sabon sansanin 'yan gudun hijira a Makurdi a yayin da wasu hukumomin ke taimaka mata wajen nemo abinci, ruwa da magani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue – Hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a garuruwan jihar Benue ya kara kamari a 'yan kwanakin nan, inda aka ce an kashe mutane sama da 100.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta rahoto cewa 'yan bindiga sun kashe sama da mutum 100, yayin da mutane sama da 6,527 suka rasa muhallansu a Benue.

Asali: Twitter
An kashe sojoji 2 a harin Benue
Jaridar The Cable ta rahoto cewa a ranar Asabar, 'yan bindiga sun kai hari Yelewata a karamar hukumar Guma, inda suka kashe mutane masu tarin yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin wannan mummunan harin, an ce mutane da dama sun jikkata, kuma sun rasa matsugunansu da cocin Katolika ta ba su matsayin mafaka a jihar.
NEMA ta tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kashe sojoji biyu da jami'in NSCDC ɗaya a wani harin kwanton bauna da suka kai masu a Daudu yayin da suke kai dauki.
'Yan sanda sun yi artabu da 'yan bindiga
Daga cikin mutane 46 da aka kai asibitoci daban daban, NEMA ta ce 20 sun mutu sakamakon munanan raunukan da suka samu.
'Yan sandan Benue sun bayar da rahoton kashe wasu maharan a wani artabu, tare da ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
A wata sanarwa da NEMA ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin, 16 ga Yuni, 2025, hukumar ta ce ana kokarin ganin an tallafawa wadanda suka rasa muhallansu.

Asali: Facebook
Mutane 5,527 sun rasa gidaje 1,069
Sanarwar ta ce hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha (SEMA), NEMA, UNHCR, Red Cross da kungiyar IOM suna kan tattara kayan tallafi da za su kai a sabon matsugunnin 'yan gudun hijira da aka kafa a kasuwae Makurdi.
"Sama da mutane 3,000, ciki har da mata da kananan yara suka rasa muhallansu kuma suke cikin tsananin bukatar abinci da sauran kayan masarufi, ruwan sha da magunguna.
"Ya zuwa daren jiya, mutane 6,527 sun rasa akalla gidaje 1,069. A cikinsu akwai mata 1,768, maza 759, yara 657 'yan kasa da shekaru 18, balagaggu 1,870, mata masu shayarwa 252, mata masu juna biyu 82 da kuma tsofaffi 91."
- A cewar NEMA.
Hari na uku a kan Yelewata a cikin mako guda ya haifar da zanga-zangar matasa a Makurdi, inda suka buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki don kawo karshen kashe su da ake yi.
Gwamna ya fallasa masu kai hare-hare Benue
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya nuna yatsa ga wasu gungun makiyaya, yana mai zarginsu da alhakin kai hare-hare masu yawa a faɗin jihar.
Gwamna Alia ya bayyana cewa waɗannan makiyaya, waɗanda ke shigowa jihar ba tare da shanu ba, sune ke da hannu a cikin hare-haren.
Gwamnan jihar na Benue ya ƙara da cewa wasu daga cikin maharan ma ba 'yan asalin Najeriya ba ne, suna shigowa ne daga ƙasashen waje.
Asali: Legit.ng