'Dangote zai Samar da Ayyuka ga Matasa a Shirin Raba Mai Kyauta,' Masana

'Dangote zai Samar da Ayyuka ga Matasa a Shirin Raba Mai Kyauta,' Masana

  • Matatar Dangote ta bayyana cewa sabon tsarin rarraba fetur da dizil zai rage hauhawar farashi da kuma samar da dubban ayyukan yi
  • Kamfanin na shirin tura manyan motoci 4,000 da ke amfani da iskar CNG domin sauƙaƙa jigilar mai zuwa sassa daban-daban na ƙasa.
  • Masana sun ce wannan mataki zai rage dogaro da masu shiga tsakani, ya kuma daidaita farashin mai, musamman a yankunan karkara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matatar Dangote ta bayyana cewa sabon tsarin da za ta kaddamar na rarraba mai fetur da dizil zai taimaka wajen rage hauhawar farashi da kuma kara ayyukan yi a fadin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa tsarin zai bai wa masu gidajen mai, kamfanonin sadarwa damar samun kaya cikin sauki.

Kara karanta wannan

Sarki ya shiga uku, bayan dakatar da shi, an tura shi gidan yari kan kalaman ɓatanci

Dangote zai samar da ayyuka wajen raba mai kyauta
Dangote zai samar da ayyuka wajen raba mai kyauta. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

A rahoton da Punch ta wallafa, bangaren sufurin jiragen sama da sauran manyan masu amfani da man fetur ma za su samu damar samun mai tare da jigilar sa kyauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ribar da za a samu wajen raba mai kyauta

Sanarwar ta bayyana cewa kamfanin na shirin amfani da manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar CNG domin rage dogaro da masu shiga tsakani da kuma inganta tsarin jigilar mai.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan kasuwa ke nuna fargaba cewa za su rasa ayyukansu sakamakon tsarin.

Wani malamin jami’a, Dr. Abimbola Oyarinu, ya bayyana cewa matakin na Dangote zai iya karɓe ikon da wasu masu ruwa da tsaki ke da shi a harkar rarraba mai.

Oyarinu ya yi zargin cewa a baya 'yan kasuwar sun kasance suna amfani da wannan damar wajen cin moriya ba bisa ka'ida ba.

Malamin jami'ar ya ce:

“Idan tsarin ya haifar da saukin farashin mai, tabbas zai rage hauhawar farashi, ganin cewa kudin mai da canjin kudi su ne manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi a Najeriya,”

Kara karanta wannan

Tinubu ya sa rana, zai ziyarci Binuwai bayan kisan kusan mutum 200

Dangote: Za a rage farashin mai a karkara

Wani masani a fannin makamashi, Ibukun Phillips, ya bayyana wannan sabon tsarin a matsayin “juyin juya hali” da zai canja yadda ake rarraba mai a kasar nan.

Ya ce:

“Yawanci mazaunan karkara na biyan kudin mai fiye da na birane. Wannan tsarin zai iya farfado da gidajen mai da suka dade ba a amfani da su, ya kuma daidaita rarraba shi a ƙasar,”

Ya ƙara da cewa aƙalla Dangote zai dauki direbobi 8,000 aiki domin fara aiwatar da wannan tsari a fadin Najeriya

Dangote zai habaka tattalin karkara saboda jigilar mai kyauta
Dangote zai habaka tattalin karkara saboda jigilar mai kyauta. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Dangote na cike gibin da gwamnati ta bari

Masani a fannin makamashi, Kelvin Emmanuel, ya ce matakin Dangote na ɗaukar nauyin jigilar mai zai bai wa ‘yan Najeriya damar cin gajiyar tace mai a cikin gida.

Ya ce matsalolin da suka dabaibaye tsarin jigilar mai tun da dadewa sun hada da rashin tsari da cikas daga hukumomin gwamnati, kuma Dangote na ƙoƙarin gyara waɗannan matsaloli.

Kamfanin Dangote zai kawo sauyi a harkar mai

Kara karanta wannan

Kisan Benue ya girgiza Najeriya, Kwankwaso, Pantami, Saraki sun yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya ce nan gaba kadan zai kawo gagarumin sauyi a harkar man fetur a Najeriya.

Aliko Dangote ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai bayan shugaba Bola Tinubu ya ziyarci matatar shi.

Matatar Dangote ta yaba da matakin gwamnatin Najeriya na cigaba da sayar mata da danyen mai da Naira domin farfado da tattalin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng